ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsofaffin Ɗaliban BUK Sun Yaba Wa Masarautar Hausawan Turai Kan Naɗa Ma’ajin Hausawan Turai

by Muhammad
1 year ago
Alh. Hassan Baita Ubawaru (Ma'ajin Hausawan Turai)

Alh. Hassan Baita Ubawaru (Ma'ajin Hausawan Turai)

Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da haɗin guiwar Tsofaffin ɗaliban Sashen Nazarin Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero Kano ajin shekara ta 2015 ta miƙa sakon godiya ga Masarautar Hausawan Turai da ke birnin Paris na ƙasar Faransa da Mai Martaba Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajou Djankaɗo, bisa naɗi ɗan wannan ƙungiya kuma shugabanta, Alhaji Hassan Baita Ubawaru a matsayin Ma’ajin Hausawan Turai a ranar Lahadi 14 ga Yulin 2024.

Muhammad Bashir Aminu lokacin da yake miƙa wa Ma'ajin Hausawan Turai kyauta a madadin Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Jami'ar Bayero aji na 2015.
Ma’ajin Hausawan Turai, Alh. Hassan Baita Ubawaru, yana karbar kyauta daga Muhammad Bashir Aminu

Sakataren ƙungiyar, Muhammad Bashir Amin ne ya aike da wannan saƙon a madadin kungiyar ga Masarautar Hausawan Turai da Mai Martaba Alh. Sirajou Djankaɗo a wajen taron walimar taya murna da karramawa da abokan Mai girma Ma’ajin Hausawan Turai suka shirya masa a birnin Kano a ranar Litinin 29 ga Yulin 2024.

  • Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
  • Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani

A jawabin na Muhammad Bashir, ya ce tabbas an ajiye ƙwarya a gurbinta bisa zaɓo mutum mai nagarta da amana da hidimtawa a al’umma irin Alh. Hassan Baita Ubawaru, a wannan matsayi kuma uwa uba daman shi Hassan ɗin masani ne a fannin ilimin harshe da adabi da al’adun Hausawa don kuwa ya samu shaidar digirinsa na farko a harshen Hausa.

ADVERTISEMENT
Ma'ajin Hausawan Turai yana karbar kyauta daga Muhammad Bashir Aminu
Ma’ajin Hausawan Turai yana karbar kyauta daga Muhammad Bashir Aminu

“Haƙiƙa an karrama mu kuma mun ji daɗin wannan karamcin ƙwarai da gaske, kuma ƙungiya za ta ci gaba da ganin wannan karamcin har abada, za kuma mu kyautata alaƙa mai kyau da wannan Masarauta ta Hausawan Turai ta fuskar bunƙasa harshe da adabi da al’adun Hausawa da taimakon mabuƙata ” cewar Muhammad Bashir.

Sakataren ƙungiyar a ƙarshe ya aike da sakonsa na taya murna a madadin mambobin kungiyar ga sabon Ma’ajin Hausawan Turai, Alh. Hassan Baita Ubawaru, bisa naɗa shi a wannan matsayi na sarauta mai girma da Allah ya sa ya zama mutum na farko a tarihi da aka naɗa a Masarautar Hausawan Turai.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

Bashir ya yi fatan Ma’ajin Turai ya ninka ayyukansa na alheri da ya saba da kuma yin haƙuri da hidimar jama’a da taimakon mabuƙata, ya kuma yi addu’ar Allah ya kama masa, ya taya shi riƙon kafa tarihi na alheri a wannan Masarauta mai girma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
Adabi

Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)

September 26, 2025
Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
Al'adu

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

September 2, 2025
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A

August 15, 2025
Next Post
Zanga-zanga: Shugaban Majalisa Ya Roki ‘Yan Nijeriya Su Kara Ba Wa Tinubu Lokaci 

Zanga-zanga: Shugaban Majalisa Ya Roki 'Yan Nijeriya Su Kara Ba Wa Tinubu Lokaci 

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.