Yusuf Shuaibu" />

Tsoho Ya Gurfana A Kotu Bisa Yi Wa Diyarsa Ciki

A ranar Litinin ce, wani dattijo mai suna Ibrahim Yunusa dan shekara 72 da haihuwa, ya gurfana a gaban kotun Jihar Gombe, bisa yin lalata da kuma yi wa diyarsa ciki. Shi dai Yunusa ya na zaune ne a Dadinkowa da ke cikin karamar hukumar Yamaltu/Deba ta jihar, ya dai musanda laifukan da a ke tuhumar sa da shi.

Alkali mai shari’a Daura Sikkam, ya bayar da umurnin a cigaba da tsare shi a gidan yari, sannan kuma ya dage sauraron wannan kara har sai ranar 13 ga watan Nuwamba, domin bai wa ‘yan sanda damar gudanar da cikakken bincike.

Tun da farko dai, an karanta bayanan farko na rahoton ‘yan sanda ta bakin magatakardar kotun, Dalaky Wanma, ya bayyana cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifin ne a lokuta da dama a tsakanin watan Disambar shekarar 2018 da kuma watan Janairun shekarar 2019. Ya ce, Yunusa ya tursasa wa yarinyarsa mai shekaru 17, inda ya yi lalata da ita har ta samu juna biyu a gidansa. Magatakardar kotun ya kara da cewa, wannan laifi ne da ya saba wa sashe na 390 da 282 na dokar fanal kot.

Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, Sajan Baka Shekari, ya bayyana wa kotu cewa, a halin yanzu ‘yan sanda su na gudanar da binciken lamarin. Ya bukaci kotu da ta dage sauraron wannan kara, domin bai wa ‘yan sanda damar kammala bincike tare da samun shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar.

Exit mobile version