Tsohon Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad (mai ritaya), ya rasu.
Wata majiya ta ce ya rasu ne da safiyar ranar Talata a wani asibiti da ke ƙasar Saudiyya.
- Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
- ‘Yansanda Sun Cafke Masu Gadi 2 Kan Satar Mota A Bauchi
Ƙungiyar Ɗaliban Shari’ar Musulunci ta Nijeriya (NAMLAS), hedikwatarta ta ƙasa da ke Abuja, ita ma ta tabbatar da rasuwarsa cikin saƙon ta’aziyya da ta wallafa.
NAMLAS, ta bayyana Marigayi Mai Shari’a Muhammad a matsayin alƙali mai gaskiya, tawali’u da jajircewa wajen aiki.
Ƙungiyar ta ce rasuwarsa babban rashi ne ga ɓangaren shari’a a Nijeriya da kuma ƙasa baki ɗaya.
A cewar ƙungiyar, ya kasance mutum mai adalci, jarumtaka da bin doka da oda tsawon rayuwar da ya yi wajen gudanar da aikinsa.
Sun ce kyawawan ayyukansa da halayyarsa za su ci gaba da zama abin koyi ga al’umma.
NAMLAS ta kuma ce ba wai Alƙali ne kaɗai ba, har ila yau Marigayi Ibrahim Tanko Muhammad ya kasance mai ba da shawara kuma tamkar uba ga ɗaliban shari’ar Musulunci da dama a faɗin Nijeriya.
Ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, ɓangaren shari’a da al’ummar Nijeriya, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.
Marigayi Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya shafe shekaru da dama yana aiki a ɓangaren shari’a, inda daga bisani ya zama Babban Alƙalin Alƙalan Nijeriya kafin ya yi ritaya.














