Tsohon kocin Super Eagles kuma gwarzon ƙwallon kafar Nijeriya, Christian Chukwu, ya rasu yana da shekaru 74.
Abokinsa nkuma tsohon É—an wasan Super Eagles, Segun Odegbami, ne ya tabbatar da rasuwarsa a safiyar ranar Asabar.
- Kallo Daya Mutum Za Yi Min Ya Gane Masana’antar Kannywood Ta Canza Rayuwata -Farida Abdullahi
- Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
An haifi Chukwu a ranar 4 ga watan Janairu, 1951.
Shi ne ya jagoranci Nijeriya ta lashe kofin Afrika a 1980 a matsayin kyaftin.
Ya kuma taka muhimmiyar rawa a nasarar Nijeriya a gasar AFCON a 1994 da kuma halartar gasar cin kofin duniya karo na farko a Amurka.
Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin É—aya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp