Shugaban Tarayyar Sobiet na karshe Mikhail Gorbacheb, ya mutu yana da shekara 91. Mista Gorbacheb, wanda ya karbi ragamar mulki a 1985, ya yi fice wajen bude kofofin tsohuwar Tarrayar Sobiet da kuma kusancinsa da kasashen Yamma, amma ya kasa hana kasarsa rugujewa a 1991.
‘Yan kasar Rasha da dama sun dora alhakin rugujewar Tarrayar Sobiet a kan manufofinsa na kawo sauyi. Jami’an asibitin da ya mutu sun ce ya yi fama da doguwar rashin lafiya. Shugaban kasar Rasha, Bladimir Putin, ya bayyana alhininsa game da mutuwar Mista Gorbacheb, kamar yadda mai magana da yawunsa Dmitry Peskob ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Rasha Interfad a cewar Reuters.
- Bukatar Samar Da Isasshen Taki Cikin Sauki Ga Manoma
- …Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai
Mista Gorbacheb ya zama babban sakataren jam’iyyar gurguzu ta tsohuwar Tarayyar Sobiet da kuma shugaban kasa yana da shekara 54.
A wancan lokaci shi ne mamba mafi karancin shekaru a majalisar da ke mulki da aka fi sani da Politburo, kuma ana kallonsa a matsayin matashi mai kwarjini, bayan shekarun da aka shafe ana samun shugabannin da suka tsufa.
Manufarsa ta bai wa al’ummar kasar damar bayyana ra’ayoyinsu ciki har da sukar gwamnati wanda wani abu ne mai wuya a baya. Sai dai ta sa yankuna da dama sun fara neman ‘yancin kai, wanda a karshe ya kai ga rugujewarta.
A matakin kasa da kasa ya cimma yarjejeniyar takaita amfani da makamai tsakanin kasarsa da Amurka, kuma ya ki shiga tsakani a lokacin da kasashen gabashin Turai suka yi wa shugabanninsu masu ra’ayin gurguzu bore.
Kasashen yammacin duniya na kallonsa a matsayin wanda ya jagoranci yadda za a kawo karshen yakin cacar[1]baka.
An ba shi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 1990, saboda rawar da ya taka wajen kawo sauye[1]sauye a dangantakar da ke tsakanin kasashen Gabashi da na Yamma.
Sai dai a sabuwar Rashar da ta bayyana bayan 1991, ya nesanta kansa daga harkar siyasa inda ya mayar da hankali a kan ilimi da ayyukan jin kai.
Ya yi yunkurin komawa fagen siyasa a 1996, amma kashi 0.5 na kur’iun da aka kada ne ya samu a zaben shugaban kasa. A shekarun baya-bayan nan ya rika fama da rashin lafiya kuma an rika jinyarsa a asibiti.
Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ce za a binne shi a makabartar Nobodebichy da ke birnin Moscow, inda a nan ne ake binne fitattun ‘yan kasar, kusa da matarsa Raisa wadda ta mutu a 1999.