Mahdi M Muhammad" />

Tsohuwa Ta Bayyana Dalilinta Na Sanya Takunkumin Rufe Hanci A Goshi

Wata mata ‘yar kasuwar jihar Ghana da ke yawan sanya takunkumin rufe hanci a fuskarta a goshi ta bayyana cewa tana sane cewa ba wurin da ya dace ba ne a sanya amma tana yin hakan ne domin samun sauki.

An ga tsohuwar matar ne tana sanye da abin rufe hanci a goshinta a kasuwar Madina da ke Accra, kuma manema labarai sun tunkare ta, inda matar ta bayyana cewa tana sanya abin rufe hancin a goshinta ne kawai da rana.

Ya ce, “Da safe lokacin da zan fara aiki, na kan yi amfani da shi wajen rufe bakina da hanci, amma da rana sai ya jike da gumi da wari don haka sai na tura shi a goshina.”

Dangane da karuwar cutar korona, babu wata tantama cewa Nanaday da wasu da ke sanya abin rufe fuska ta hanyar da ba ta dace ba za su fallasa kansu ga cutar.

Kwararrun masanan kiwon lafiya suna ci gaba da cewa, sanya maskin a kowane lokaci na iya haifar da matsala idan ba a yi shi yadda ya kamata ba.

A wani labarin kuma, wani fasto dan kasar Ghana ya bayyana irin matan da yake ganin duk wani na miji mai son zaman lafiya dole ne ya guji auren su.

A cewar babban faston cocin Grace Mountain Minista, Fasto Elbis Agyemang, akwai wasu halaye guda goma da dole ne maza su lura da su yayin da suke neman matar da za su aura don gujewa yin saki a nan gaba.

Ya yarda cewa, mai yiwuwa ba nufin ma’aurata ne su yi saki ba, amma wasu halaye na iya wajabta hakan idan ba a kula da su ba a farkon fara maganar aurensu, kafin daga karshe su yanke shawarar yin aure.

A ganinsa, ya fi kyau a fasa bikin aure mako daya ko kwana biyu kafin bikin, maimakon a yi auren da daga baya zai haifar da babban abin kunya daga tare da lamura masu rikitarwa da yawa.

 

 

Exit mobile version