Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, musamman Zamantakewar Aure, Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. A yau ma shafin na tafe da tattaunawa kan wani sako da ya ci karo da shi game da cin amana.
Ga sakon: “Na yi tafiya na tsawon shekaru shida, na bar ‘Yata me shekaru takwas a wajen kanwata. Ina biya mata kudin makaranta tare da ‘ya’yan kanwar tawa guda biyu duk da cewa tana da aure. A kowanne wata nakan tura wa kanwata dubu saba’in na ciyarwa da sauran hidimomi, wani lokacin ma har dubu dari dan kawai na tabbatar da ‘Yata ba ta rasa komai ba, ita ma kanwata haka. Na bude wa kanwata wurin sana’a don kawai in tabbatar tana cikin walwala, saboda mu biyu ne kawai muka rage. Haka nan na siya wa kaina filaye guda biyu, sai kuma wani fili mai girman gaske wanda na shirya gina gida biyu daban-daban, daya na kanwata daya kuma nawa, kamar dai gidan dangi. Yaran kanwata su ne manya, nakan kira waya ta hoton bidiyo mu yi magana da ‘Yata, wanda hakan ya ba ni damar gane cewa ‘Yata tana cikin wani hali. Ban sanar da su zan zo ba, don ina son in yi musu ba-zata, kawai na hau jirgi na taho Nijeriya. Kwatsam ina shiga gida sai na tarar da kanwata tana dukan ‘Yata da ‘belt’ wai saboda ta jira ruwan sama ya dauke kafin ta dawo gida. Ni ban sani ba, ashe tuni kanwata da ‘ya’yanta sun mayar da yarinyata baiwarsu, suna saka ta duk wani aikin gida, har ta kai ta makaranta mai nisa kuma me arha, duk da irin kudaden makarantar da nake turawa, ‘Yata ba ta cin abinci mai kyau, duk kayan da na turo mata masu kyau kanwata ta kulle su a akwati tana bai wa ‘Yarta ta saka, ya yin da ‘Yata kuma take saka tsumma. Duk kudin da nake tura wa kanwata don kar na wahalar da ita amma sau daya take ba ta abinci a rana, yanzu da na mutu kuma fa, wane irin riko za ta yi wa ‘yata? A gaskiya ina ji a raina cewa ba zan iya yafe wa kanwata ba. Hatta mijinta ya sha yin fada a kan abubuwan da take yi amma ba ta ji. Yanzu haka ina tunanin hukuncin da ya dace na yanke a kan kanwata saboda kamar yadda na fada mu biyu kawai muka rage uwa daya uba daya a duniya? Idona ya rufe, amma don Allah jama’a ku taimake ni da shawara!”
Dalilin hakan shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannn batu, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Sadiya Garba (S.Girl) Jihar Kano:
Hmm.. Kaico an ci amanar zumunci, ai maganar yafiya ba ta taso ba, saboda ba ta duba zumunci ba ta ci Amana kuma ita ta aikata abubuwa da dama, wadanda Allah ya yi hani da su; Na farko ta ci amanar zumunci, na biyu tayi zambo cikin aminci, na uku an amince mata tayi ha’inci da sauransu. Kawai ta rabu da ita kunya ma ta isheta domin wallahi ko a haka ma ba za ta taba jin dadin rayuwarta ba sai ta tsangwami kanta, dama ai karshen zalunci nadama ne. Sannan dabi’ar manzon Allah (saw) ma ya yi Allah wadai da masu hali irin nata domin tayi zambo cikin aminci ne, dan haka masu irin wannan dabi’a ku ji tsoron Allah, ku sani azabar me cin Amana daban take musamman ma akan zumunci, duba da yadda ta aminta da ita Amma ta biye wa son zuciya da rudin shaidan ta aikata abin da zai zo ya zamar mata dana sani. Ya ubangiji Allah kayi mana tsari da cin Amana, da kuma sharrin zuciya.
Sunana Yakubu Bala Gwammaja:
Abin da zan yi mata shi ne; zan gaya mata abin da na gani, gaskiya idan na bar ta a raina zan dinga ganinta da abun a raina ba zan yafe mata ba, idan ni ne zan dauke ‘ya ta na bata kulawar da ya kamata ko nayi sauri nayi auren mace mai san yara. Na dan janye tallafin ga kanwata, ko hakan zai sa tayi hankali ta gyara.
Sunana Lawal Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA Yalwa KNARDA:
Shawarata anan matakin da aka dauka yayi tsauri duba da ‘yar uwa ce ta jini kuma su kadai suka rage a duniya wanda suke ciki daya, amma gaskiya ta ci amana, amma tunda ita ce karama kuma ba tada hali sosai kawai kamar yadda aka dauke ‘yar a yafe mata, amma duk wani batu na taimako sai a janye hannu ko za ta gane gaskiya ta daina cin amana, tunda Allah yana son masu yafiya idan anzalunce su, sannan a nuna wa diyar abin da ya faru ya wuce kada ta yi wa Antinta da yaranta kallon sun zalunce ta, amma a karshe dai ina mai bata shawara da a yafe mata hakan ma zai sa ta cikin tunani, wanda za ta daina koma ba akan ‘yar uwar ta ta ba, anan gaba. A kira ta su zauna ayi mata nasiha ta ji tsoron Allah a duk inda take da ma sauran mutane maciya amana irinta. Shawarata anan ita ce mu rinka jin tsoron Allah a duk inda muke, sannan ita fa amana ba wai ta kudi ko ta kadara ce ba, balle idan muka tabbata za mu gane cewa mun ci amana. Hatta yaran da muka haifa na cikinmu Allah ma ya ce amana ya ba mu to ina ga wanda zai yarda da mu har ya ba mu amanar abin da aka ba mu, musamman ita da aka bata amanar ‘ya mace wanda yake ita ma diya mace ce, kuma ko da asirin ire-irensu bai tonuba to wallahi akwai lokacin da kowa zai gani kuma ya sani Allah ya sa mu gane kuma mu gyara mu kawar da son zuciya.
Sunana Masa’ud Saleh Dokadawa:
Shawarar anan ita ce gaskiya koda za a yafe mata sai an gama yi mata kyakyawan gargadi da kuma jan hankali akan abin da tayi ita ma ta san ba ta kyauta ba, sannan zan janye duk wani tallafi ko bada taimako na Jin kai wanda nake mata na tsawon lokaci don ita ma ta gane amfani na. Zan kira wo ta da mijinta da ‘ya’yanta, da sauran danginmu na shaida musu irin zalinci da cin amanar da suka yi min. Don kada wani ya zarge ni nan gaba. Ita kuma a san abin da ta yi min a rayuwa. Shawarar ita ce su ji tsoron Allah su daina su sani cewa Amana abar tambaya ce ranar hisabi, sannan cin amana laifi ne babba, yana kawo fushin Allah, don haka ta kiyayi gaba ta gyara halinta.
Sunana Faridat Hussain Mshelia, Suleja Jihar Neja:
Hakuri da yafiya su ne kan gaba, tunda Allah yana son bayinsa masu yafiya, ba wayon mutum bane kuma ba dabara ba ce ya sa aka fahimci ‘yar tana cikin wani hali, rashin hakki ne ya sa Allah ya nuna hakan, tunda har Allah ya kubutar da ‘yar a gode wa Allah. Shawarar da zan baiwa masu irin wannan halin ita ce su ji tsoron Allah su sani ko dabba ka ke kiwo bai kamata ka ci amanar shi ba balle mutum sukutum.
Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Ya kamata a yafe mata domin duk wanda ya yafe wa wani to shi ma sai Allah ya yafe masa kurakuransa, a rabu da ita aa dauke ‘yar, kuma a fita daga harkarta, hakan zai sa ta gane. Ta yi babban laifi a rayuwarta kuma akwai yiwuwar ta gyara halinta. Masu irin wannan halin su ji tsoron Allah su sani cewa duk abin da kayi za a yi maka irinsa, kuma dole mutum ya girbi abin da ya shuka.
Sunana Abba Gada Rano Unguwar liman Gada:
Gaskiya kanwar tayi kuskure babba kada a ki yafe mata, dan Allah yana son masu yafiya kuma Manzon Allah (s.a.w) Ya ce; Idan aka bata muku ku nuna, idan aka nemi ku yafe, ku yafe. A yafe mata a fita daga harkokinta gaba daya. Ma su irin dabi’ar su ji tsoron Allah su daina Allah ya yi hani da zalunci.
Sunana Maryam Hussain Zariya:
Shawarata shi ne a yafe mata Allah yana san mai yafiya. A rage yi mata alkhairi saboda rowa babu kyau. Masu irin halin su ji tsoran Allah su san cewa kamatudinu Tudan.
Sunana Muktar Adakawa:
Hakuri ya kamata a yi domin jini daya ya fi karfin wasa, dole nan gaba za ta gane gaskiya, Ita yarinyar ta ta wanne mataki za a dauka akanta. Ya kamata a yafe mata, amma a janye jiki da ita har sai ta gane kurenta.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi (Dr. Haibat):
A gaskiya wannan ‘yar uwa ta shiga hakkin ‘yan uwantaka, sannan za ta ja wa kanta zagi bakin mutane ire-iren wannan matsala ko hali, ba shi da amfani duk wanda ya taimake ka ya gama yi maka komai a rayuwa, ballantana kuma a ce jininka na ‘yar uwata, Allah ya sa mu dace ya kamata a yafe mata ko ba komai uwa daya ta fi karfin wasa, idon mutanen duniya ma kadai ya ishe ta tunani, sannan idan akwai ra’ayin ci gaba da taimaka mata dan Allah a ci gaba ba dan halinta ba, sai dan iyayensu, sannan kuma duk mai irin wannan hali to ta gyara ko dan gobenta ya yi kyau, duk wadda ya taimaki wani shi ma Allah zai taimake shi, mijinta kuma Allah ya ba shi hakurin zama da ita ko dan yaransu.
Sunana Yahya Salisu:
A ganina a yafe mata tunda ‘yar uwa ce, a janye duk wani tallafi/gudunmawa da ake bata tunda ba ta da amana. duk mai irin wannan halin ya ji tsoron Allah ya daina domin har a wajen Allah laifi ne kuma cin amana ne.
Sunana Usman iliyasu Majidadi Kano:
Duk da an kasance mai ikon daukar mataki a yafe mata tunda Allah ya sa an gane kafin lokaci ya kure, Zumunci abu ne mai muhimmanci. A karbe ‘yar a kuma ci gaba da kulawa da yaranta ai kanwar ce ta yi laifi ba su ba, matukar don Allah ake yi ai ba za ta fasa ba. Duk mai irin wannan halin farkon da kansa ya san bai da kwanciyar hankali ko asirinsa bai tonu yau ba ranar lahira zai iya tonuwa don haka ya ji tsoron Allah amana abu ne mai girma.
Sunana Abdullahi Mai Nasara Jihar Kano Nassarawa LGA Birgade Gama-C:
Ah to! ni dai shawarar da zan iya bayarwa ita ce; tunda har ta kasance kanwa ce to bai kamata a ce an watsar da ita ba, kawai dai a dauke ‘yar daga wajanta, kuma a janye mata dukkan wani tallafi da take yi mata, amma har sai ta gano kuskurenta, kuma ta nemi gafarar abin da ta aikata mata amma du da haka kar a sake daukar amana a damka mata har abada. Abin da ya kamata a yi mata shi ne; a janye dukkan wata hurda da ita, amma bangaren tallafawa kuma a nesance a sosai har sai tayi nadamar abin da ta aikata. Shawarata ga masu irin wannan dabi’ar ita ce su tuna cewa duk abin da ka shuka na alkairi ko na sharri babu shakka sai ka girbi kayanka, kuma kar su manta idan hakan akan ya ‘yan su ta kasance yaya za su ji a ransu, ubangiji ka bamu ikon iya rike amana tare da tausayin na kasa da mu.
Sunana Fatima Jameel Yusuf Kofar Na’isa:
Tab-di-jam! Gaskiya ba ta kyauta ba, amma ayi hakuri kar a biye mata, a duba zumuncin da ke tsakaninsu a yafe mata, domin bahaushe ya ce hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar, a nuna mata kuskurenta domin idan aka barta ai ba za ta taba gyarawa ba, sai ta zaci ko tsoronta take ji ba za ta iya daukar hukunci akanta ba. gaskiya dai me irin wannan dabi’a ta ji tsoron Allah, domin shi ubangiji baya yafe hakkin wani akan wani, shi me yafiya ne, amma tsakaninsa da bawansa.
Sunana Ibraheem Isma’el Ibraheem daga Jihar Kano Jogana:
Gaskiya a tunani na abin da ya faru da ‘yar nan kaddara ce ga ‘yar da kuma me ‘Yar, gaskiya kanwar ba ta kyauta ba, kuma hausawa sun ce ka gina ramin mugunta daidai da kai dumin watarana kai zaka fada, kuma ubangiji yana cewa; “innal laha ma assabirin” Allah yana tare da mai hakuri, idan aka yafe mata ‘may be’ ta iya daukar izina, Allah ya shirye ta ta gyara halayanta. Kuma a yi mata nashiha cewa; “idan kin mutum yayin da ki ka bada rikon wadannan ‘ya’yan naki ko ki ka yi tafiya ki ka zo ki ka tarar da su za ki ji dadi”, ki yi mata nasiha yin hakan zai sa ta shiryu idan Allah ya yi tana da rabo, Shawara ita ce duk abin da baka so kar ka so ka yi wa wani.