Biyo bayan harin da aka kai a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja da kuma bayanan sirri kan harin da aka shirya kai wa a harabar filin sallar idi a ranar Asabar din 2022, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta haramtawa motoci shiga duk wani filin sallar idi da ke Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Babaji Sunday, ne ya bayyana hakan a cikin sakonsa na Sallah ga mazauna babban birnin tarayya Abuja.
- Hukumar Gidan Gyara-hali Ta Nijeriya Ta Tabbatar Da Harin Gidan Yarin Kuje, Abuja
- Wani Abun Fashe Wa Da Ake Zaton Bom Ne Ya Tashi A Gidan Yarin Kuje Da Ke Abuja
Kwamishinan ya kuma kara da cewa, a kokarin cimma matsaya guda na tabbatar da tsaro, rundunar za ta kara tsaurara matakan tsaro da ayyukanta na bincike.
Jami’an ‘yan sanda da ke sa ido kan wuraren ibada, wuraren shakatawa da wuraren zaman Jama’a da kuma mayar da martani cikin gaggawa. ga duk wani kira na damuwa daga ko’ina cikin Abuja.
Wani bangare na sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, DSP Josephine Adeh, ta ce, “Musulmin da za su so gudanar da Sallar Idi a filin Sallar Idi na kasa da ke kan titin filin jirgin, su lura cewa akwai isasshen fili da aka ware, ana kira da Jama’a da su guji yin Sallah a kan titin mota domin tabbatar da tsari da tafiyar da zirga-zirga yadda ya kamata, haka nan kuma za a ringa faka ababen hawa a gadar Dantata daga karfe 7:00 -10:00 na safe.
“A cikin haka motocin banza ba za a bari su yi fakin a gaban filin sallah ba a kan titin mota.
“A duk sauran wuraren da ake yin addu’o’in da ke cikin babban birnin tarayya Abuja, babu wata mota da za a ba da izinin yin fakin tazarar mita 200 a kusa da filin sallah. Don haka ana shawartar masu ibada da mazauna wurin da su ba jami’an ‘yan sanda da aka tura hadin kai don aiwatar da su.”
CP ya kara da cewa, an yi amfani da dabara da kuma kadarori na rundunar ta hanyar dabara a cikin lunguna da sako na yankin domin dakile duk wani laifi ko barazana ga rayukan mazauna yankin.
Hakazalika ya nanata kudurin rundunar na yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da kuma ‘yan kasa wajen inganta tsaron jama’a, zaman lafiya da tsaro a babban birnin tarayya Abuja.