Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

TUMBIN GIWA: Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnoni Ga Tsoro Ga Takalar Faɗa

by Tayo Adelaja
October 11, 2017
in NAZARI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da El-Zaharadeen  Umar 08029073523

Ƙaramar hukuma ita ce gwamnati mafi kusa da talakawa, ita ce hukuma da take fara kula da duk wani sha’anin da ka iya tasowa musamman ga mutanen karkara, ita fata na kusa-kusa ga mutane wajan miƙa koƙensu tare da tsammnin samun biyan buƙata, ita uwa ma bada mama ga kowane ƙaramin ma’aikaci, ita ce tushe na aikin gwamnati, kai ita ce ma gwamnatin baki ɗaya.

samndaads

Abinda yasa na fara zayyana abubuwan nan shi ne, babu wani abu a boye game da ƙananan hukumomi a wannan lokacin da aka yi watsi da su, aka maida su wani wurin zubar da ma’aikata, inda ake ganin ma’aikacin ƙaramar hukuma kamar wani almajiri ko wanda aka taimaka mawa domin ya samu abin sawa abakin salati.

An maida ƙaramar hukuma wani wurin haɗuwa a gaisa kowa ya kama gabansa, an ɗauka duk mai aiki a ƙaramar hukuma shi ne mutun mafi ƙasƙanci a cikin ma’aikata, ba a kallon mutun da ƙima ko daraja indai a ƙaramar hukuma ya ke aiki.

Gwamnatoci da ‘yan siyasa da masu riƙe da madafun iko da masarautun gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin ƙananan hukumomi sun samu kansu a wannan hali da muke magana akai, saboda cimma wani gurinsu na duniya ko kuma na siyasa da neman mulki.

To, amma fa, duk da haka, ƙaramar hukuma ita ce gwamnati mafi kusa da kuma tasiri wanda ta zama abin dogaro a siyasance, kai akan kowane irin batu, ‘yan siyasa sun fi kowa sanin haka, musamman waɗanda suka taɓa hawa madafun iko.

Tambaya anan, me yasa aka yi watsi da wannan mahimmin wuri da ke taimakawa al’umma da kusan kashi 75 da al’ummomi, me ake nufi da haka, ba su da sauran mahimmanci ne ko ko, wake da sa hannun wajan faruwar hakan, me ake son  cimmawa aka bar su suka koma haka, me hakan zai haifar a nan gaba, wane tunani ake da shi ga waɗanda ake shugabanta a ƙananan hukumomi?

Gwamnoni da ‘yan siyasa sune kanwa uwar gami da kuma sanadiyar komawar ƙananan hukumomi haka saboda dalilan siyasa da suke amfana da su, amma saboda tsabar ƙeta da rashin tausayi kulin da ƙananan hukumomi ake yaudarar talakawa wajen cimma gurin siyasa.

Babu wani ɗan siyasa da zai ci zaɓe a kowane irin mataki ba tare da ƙaramar hukumarsa ta taka mahimmiyar rawa ba, amma ƙaramar hukuma ita ce suke ƙira da baƙabarta a siyasance, ma’ana duk wanda ke aikin acan, kodai bai san abinda yake ba ko kuma bashi da zaɓin da ya wuce yin wannan aikin.

A Nijeriya duk gwamnan da ya tashi buge da yaudaran siyasa, ya kan ce ƙananan hukumomi su ne gwamnatocin kusa da al’umma saboda za su yi amfani da su wajen gina jama’a ta hanyar kawo ribar dimokoradiya, hakan yana yi wa mutanen karkara daɗi, idan suka ji, ance da su, za a fara idan giwa ta faɗi.

Sai dai a mafi yawan lokuta, sune ke shan bakar wuya, sune koma baya, sune kullin suke mafarki wane sai cece su, sune kullin akan gaba wajen goyan bayan ‘yan siyasa, sune kullin ke da fatan za a yi masu maganin matsalolinsu, sune kullin ake yaudara.

Har yanzu wannan batu yana nan a matsayin shafa labari shuni. Ko yaushe talakwa za su fara ɗaukar mataki, domin yi wa tufkar hanci?, ya kamata ace ‘yan siyasa sun bullo da wata sabuwar hanyar yaudara, ba kullin za a yi zaɓen ƙananan hukumomi ba amma shiru kamar an aika Bawa garinsu.

Arewacin Nijeriya ake da wannan fatan da kuma sa rai, amma jahohin kudancin ƙasar nan  babu wani Gwamna da zai yaudari jama’a da maganar zaɓen ƙananan hukumomi sai dai ya zo da wani sabon salon yaudarar.

Tuni suka fara mantawa da wani abu wai shi zaɓen ƙananan hukumomi saboda ba shi ke gabansu ba, kuma ba da shi suka yaudari mutanen su ba, amma me yasa wasu gwamnoni a arewa suke jin tsoron yin zaɓe da zai taikamawa tafiyar siyasar su? Me zai hana su yi ƙoƙari su jaraba yin hakan ko da sau ɗaya ne.?

Yanzu abinda ke faruwa shi ne kowane gwamna idan ya ɗare akan kujerar mulki sai ya yi ƙoƙarin maida ƙananan hukumomi a matsayin wani makami da zai riƙa amfani da shi domin cin karansa ba babaka, da an motsa sai ya ce zai yi zaɓen ƙananan hukumomi.

Sai dai kuma an kasa gane wane tsoro ne yake hana su yin zaɓen, bayanai sun nuna cewa da yawa gwamnonin yanzu sun yi wa jama’a laifi da dama kuma sun kasa ba su hakuri ko kuma su yi masu aikin da za su manta da abinda ya faru, shi yasa suke da shakku cewa da an yi zaɓe babu abinda zai hana su dafa ƙasa.

Wasu kuma na ganin lokaci bai yi ba da za a yi haka ba, suna jiran a buga gangar siyasa sai su yi amfani da wannan damar su ƙara yaudaran jama’a da suna zaɓe, ta inda za su ƙara kafa mutanen su a cikin siyasa domin amfanin gaba.

Akwai masu ra’ayin cewa ba za a yi zaɓen ba, saboda matsalar ƙarancin kuɗi da ƙananan hukumomi suka fuskanta daga kuɗaɗan da gwamnatin tarayya take ba su na kason arzikin ƙasa na wata-wata, saboda haka sai ranar da aka yi magani wannan matsala sannan za su yi zaɓe.

Kazalika wasu nan gani lokaci bai yi ba da za su nuna ƙwarin ƙashinsu ba, saboda haka akwai sauran lokaci inda za su shirya tsaf sannan su tunkari wannan baban ƙalubale, su kuma yi abinda suka saba yi na ƙwace da kama karya da murɗiyarzaɓe domin a cimma nasara.

Babu shakka talakawan da ake yi wa baba rudun sun fara farkawa daga dogon barcin da suke yi, tare da fara sabon shirin da kuma dakun masu mulki su ga ta inda za su sake bullo masu da sabuwar yaudara, ko dai ta zaɓe ko kuma su zo da wani sabon.

Wannnan lamari dai ya fara zama gaba kura baya sayaki a tsakanin gwamnoni musamman na arewa ta yadda wasu sun fara lura da haka duba da irin sabon salon tafiyar da shugabancin ƙananan hukumomi da ya fara canza wa zuwa yanzu.

Wasu kuma sun daskare sai dai ko me zai faru ya faru, ga alama kuwa wani abun zai faru, sai Allah Ya kiyaye, tunda mun ga yadda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’I ya ce zai yi zaɓen ƙananan hukumomi a watan Disamba mai zuwa, amma daga baya ya yi amai ya lashe, inda ya fake da maganar sha’anin tsaro wanda ya ce ita ce babar barazanar da yake fuskanta, amma da ya shirya zaɓen

SendShareTweetShare
Previous Post

Muƙarrabai Ne Suka Ci Amanar Jonathan –Wike

Next Post

NAZARI: ‘Yar Jagora

RelatedPosts

Dan Uwan Minista

Ayyukan Ta’addanci A Arewacin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
12 hours ago
0

Ga duk mai tabaraun hangen nesa, zai fahimci cewa lallai...

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

Sarkar Da Za Ta Sarke Kaduna Bayan Amsar Bashin Dala Miliyan 350 Daga Bankin Duniya

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Dr. Nasiru Aminu “Babu al’ummar da za ta kasance...

National Economy

Shekara Daya Da Fara Fitowa: Gudumawar Jaridar NATIONAL ECONOMY Ga Tattalun Azikin Nijeriya

by Muhammad
7 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, A jiya Asabar ne jaridar NATIONAL...

Next Post

NAZARI: ‘Yar Jagora

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version