• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tun Muna Kanana Aka Dora Mu A Kan Kyakkyawar Tarbiyya —Dakta Zahra’u

byBilkisu Tijjani
3 years ago
Zahra'u

Hajiya Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ita ce Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata da cigaban al’umma ta Jihar Kano, kuma tsohuwar Mataimakiyar Kwamdan Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ‘yar Gwagwarmaya mai fafutukar kula da darajar Mata da Kananan Yara.

A tattaunawarta da Wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta bayyana matukar damuwarta Kan halin da yara Mata da kananan yara ke tsintar kansu a ciki. Ga dai yadda Tattaunawar ta kasance.

  • Gamayyar Matasan Arewa A Kudu Ta Yi Tir Da Karuwar Ta’addanci A Arewa

Za muso Jin dawa Muke tare a wannan Lokaci?
Alhamdulillahi Ni dai sunana Dakta Zahra’u Muhammad Umar Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata da cigaban al’umma Ta Jihar Kano.

Bayyanawa Jama’a takaitaccen tarihin Gwagwarmayar rayuwar ki?
Gaskiya ne ansha fama da Gwagwarmaya tun muna kanana wajen kokarin dora mu a kan kyakkyawar tarbiya, har kuma zuwa lokacin da aka samu a makarantar firamare, na yi Sakandire har kuma zuwa Jami’a tare da samun digiri har da digir-digir, na zama Mataimakiyar Kwamdan Hukumar Hisba na Jihar Kano, gashi kuma yanzu Allah cikin ikonsa ni ce Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata ta Jihar Kano.

Kasancewar ki Mace kuma gashi kina matsayin Kwamishiniya a wannan ma’aikata, shin ko ya aka samu ma’aikatar?
Alhamdulillahi Allah ya kawo ni wannan Ma’aikata kuma Alhamdulillahi na samu wannan ma’aikata cikin tsari, tana da sassa daban-daban wadanda suka hada da sashin lura da matsalar barace-barace, kangararrun yara, sashin lura da harkokin mata da sauransu, kuma ma’aikatan hukumar kowa na aikinsa yadda ya kamata, duk abinda aka basu shi suke ba wanda yake wasa da aikinsa.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

Zahra'u
Gwamnan Ganduje (a dama) tare da Dakta Zahra’u Muhammad Umar

Batun barace-barace na cikin ayyukan da suka rataya a wuyan wannan hukuma, ko ya ake kallon wannan kalubalen?
Wannan lamari shi ne babban kalubalen da wannan Ma’aikata ke fama dashi, kuma kasancewar dukkan karatuttukan da na yi a fannin addini ne, sannan duk wanda ke bibiyar hadisan Annabi Muhammad (SAW) ya sa ya hana bara, kamar yadda Allah ta’ala ya hana ta, harma Annabi yake cewa duk wanda ya mayar da barace-barace ko roke-roke zai tashi ranar alkiyama fuskarsa babu tsoka duk sai kasusuwa.
Wannan tasa a ganina ni yakamata ma nafi bayar da gudunmawa wajen hana barace-barace, saboda irin yadda addini ya nuna mana ilar bara. Amma dai saboda wannan aiki Ma’aikatar Mata kadai ba za ta iya ita kadai ba, hakan tasa na rubuta wa Gwamna shawarar samar da hukuma guda domin tunkarar wannan aiki, kuma alhamdulillahi an samar da wannan bangare kuma aiki na ci gaba yadda ake bukata.

Ina batun yara masu matsalar kangarewa, ko shaye shayen miyagun kwayoyi, shin me ake a kan Haka?
Kaji bangaren dake matukar tayar min da hankali, wanda yanzu Haka mun kammala dukkan shirye-shirye an bude cibiyar lura da masu irin waccan matsalar a garin Kiru, kuma an samar da kwararrun masana kama daga Likitoci, Malaman Jami’a da sauran masu Ilimi a wannan bangare, an bude gidan da yara 30, ana kula da abincinsu gangariya, lafiya, tsafa da duk abinda ake nema, sannan babu fita.
Muna kara yi wa Allah godiya naga faifan bidiyonsu Malam Gwanin sha’awa, harma tsoro nake kar bayan kammala samun lafiyarsu su ki yarda da komawa gidajensu, sakamakon irin rikitibar da suke sharba a wannan gidan lura da gyaran hali, kuma wani abin sha’awa ‘ya kudi kakilan ake karba wajen kula da yaran, Gwamnatin Ganduje ce ke daukar mafi yawan nauyin.

Ya ya dangantakar aiki take tsakanin ki da Ma’aikatan wannan Ma’aikata?
Ni ba abinda zance da abokan aikinna sai godiya suna yin duk abinda ake bukata, kuma kamar yadda ma’aiki ke shawarar sahabansa, haka Nima na nauki irin wannan umarni, duk abinda zan yi sai na shawarce su, hakan tasa muke aiki tare cikin nutsuwa da Jin dadi.

Gwamnatin Gwamna Ganduje ta ciki Shekara 7 da doriya, shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
Alhamdulillahi Gwamna Ganduje ya cika alkawarin da ya yi wa Kanawa harma da kari, musamman idan aka dubi yadda ya mayar da birnin Kano wani kasaitaccen birni, dubi gadojin sama da kasa sai kace a Dubai, dubi manyan Asibitoci musamman asibitin kwararru na Muhammadu Buhari dake Giginyu, dubi na yara dake titin zuwa Gidan Zoo, samar da cibiyar koya sana’u ta Aliko Dagote, Dubi Inganta Harkar
Noma, tsaro da Tallafa wa Mata da matasa a Kananan Hukumomin Jihar Kano 44 wadda Mai Dakin Gwamnan ke kai gauro ta kai mari ana saukewa Mata kabakin arzikin.

Zahra'u
Dakta Zahra’u Muhammad Umar

Wasu a batun Fidda wanda zai yi wa Jam’iyyar APC takarar kujerar Gwamna a shekara ta 2023 wasu sun yi zanton yadda masu abin hannu suka bazo zawarcin wannan kujera, kwatsam kuma sai aka ji Gwamna Ganduje ya nuna mataimakinsa, me hakan ya nuna?
“Gaskiya da rikon amana”, tsantseni da sanin ya kamata sannan uwa uba rashin kwadayin mai girma Gwamna, wannan ke tabbatar da kaunar da Ganduje kewa Kano da Kanawa, daukar mataimakinsa alama ce ta adalci, wanda kuma duk duniya an Jinjina masa bisa yakana da dattako.

Duk da kila ke ba malamar lissafi bace, amma da za’a ce ki baiwa Gwamnatin Ganduje maki, shin ko maki nawa zaki bashi?
Alhamdulillahi ba don matsalar Korona ba da maki 100% bisa 100% zan bashi, domin bayan alkawurran da ya dauka har sai da ya yi kari, domin baya cikin alkawarin da ya yi alokacin yakin neman zabe cewa zai kara yawan Masarautu a Kano, gashi ya yi, tuni wadannan garuruwan sun zama birane, kalli batun Ilimi Kyauta kuma wajibi ga kowa, ko Hasidin iza hasada ya yarda Ganduje ya ciri tuta.

Yanzu da ake tunkarar Zaben Shekara ta 2023 wadda Kuma Gawuna ne Dan Takarar Jam’iyyar APC, shin koya kike Kallon nagartar dan takarar naku?
Ai daman kyan da ya gaji ubansa, mun gamsu tare da yakinin tsayar da Gawuna wannan takara Alhairi ne ga Kano da Kanawa, ba karamin hange Gwamna Ganduje ya yi ba wajen nuna Gawuna a matsayin wanda da yardar Allah zai gaji buzunsa.

Me Kika fi sha’awar Ma’aikatan da kuka Yi aiki tare su dinga tunaki dashi?
Kyakkyawan Adalcin mu ka kwatanta tare da abokan aikinmu, sannan su kara himmatuwa Wajen dorawa inda Muka tsaya.

Mene sakon ki na karshe?
“Jama’a su kara Jajircewa wajen tarbiyar yaransu, wannan lamari shi ne yafi tsayamin a rai, ka ga Yara ana tsinto su a kwararo, wasu suce korosu akayi daga gida, Idan kuma muka gayyaci iyayen alokuta da dama sai kaga Uwar ko uban sunfi yaran bukatar taimako, Haka muke ta fama. Don Haka Ina kara kira ga iyaye a ci gaba da addu’a a tarbiyantar Yara, sai Allah ya jikanmu.

Muna godiya
Nima na gode

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
2023: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Bukaci Zulum Ya Zama Abokin Takarar Tinubu

2023: Masu Ruwa Da Tsaki A APC Sun Bukaci Zulum Ya Zama Abokin Takarar Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version