ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tunawa Da Sam Nda-Isaiah Bayan Shekara Biyar

by Abraham Nda-Ishiah and Sani Anwar
2 days ago
NDa

Abin da ke sama na nuna cewa, shekaru biyar sun shude; tun daga watan Disamba 11, 2020, zuciyata na kadawa kamar iska, tunanina na fada min kamar jiya abin ya faru. Wayata ta yi kara a farkon wadannan sa’o’in da wannan mummunar kaddarar ta faru; matarsa Zainab ce ta kira.

Muryarta a tsaye, amma cikin matukar damuwa, ta gaya min da Hausa cewa; “Mai gida ba shi da lafiya.” Ta kara da cewa, “Muna asibiti,” ma’ana “Muna asibiti.” Nan da nan na yi sauri na fita sanye da karamar riga (T-shirt) da hular wasan ‘baseball’, zuciyata cike da tsoro da fargaba.

  • Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Farfesa Ibrahim Tsafe A Matsayin Sabon Shugaban Jami’ar ZAMSUT
  • Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Da na isa asibitin, na iske Sam jikin nasa da sauki, sai ya daga kansa ya kalle ni, ya yi murmushi a sanyaye ya ce; “Kana nan.” Hakan ya kwantar min da hankali. Harry Odey, abokisa tun a jami’a, shi ma ya halarci asibitin.

ADVERTISEMENT

A daidai wannan lokaci, sai likitocin suka tabbatar mana da cewa; babu matsala, sauki nan tafe, amma duk da haka, da misalin karfe 10 na dare a wannan rana, Sam Nda Isaiah ya bar duniya. Babu shakka, na yi matukar shiga yanayi mai zafi da radadi da ya hana ni iya cewa komai sakamakon jin mutuwarsa.

Duk da cewa, shekaru biyar kenan da suka wuce, amma ainihin aiki da hangen nesan Sam, na ci gaba da yin tasiri sosai a kan iyalansa, al’ummarsa da kuma kasarmu baki-daya. Lokacin da muka fuskanci wannan rashi, mun samu sauki ta hanyar samun ta’aziyya da nassoshi daga littafi mai tsarki da ke tunatar da mu cewa; “duk wanda ya yi aiki mai kyau, zai samu kyakkyawan sakamako, wanda kuma ya yi akasin haka, ba za a sake jin duriyarsa ba”, (Misalai 10: 7 KJB). Sam ya yi rayuwa mai cike da adalci da aiki tukuru.

LABARAI MASU NASABA

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

Na tuna da wani labari da na saurara daga Boss Mustapha, wanda a wancan lokaci shi ne sakataren gwamnatin tarayya (SGF). Labarin a kan wani mutumin Sam ne. Sam ya fada wa mutumin cewa ya same shi ranar Juma’a. Daga bisani, sai ya kara aika wa da mutumin sakon tes, domin tunasar da shi zuwan nasa, ko da kuwa yana kwance a gadon asibiti ne. Ko shakka babu, mutum ne mai matukar kulawa da tausayi har zuwa lokacin karshe na rayuwarsa.

Washegari Boss, ya yi matukar kaduwa da jin cewa; Sam ya bar duniya. Yana ta hira da Sam, bai san yana asibiti ba har ya mutu.

Kwana daya kafin rasuwarsa, Sam ya jagoranci bikin kakkamar da kwamitin masana tattalin arziki na kasa, taken da ke kan LEADERSHIP. Ya ba da gudunmawa a bangaren ayyuka, ya kirkiri taswirar hangen nesa, ya kuma sadaukar da kai har zuwa karshen rayuwarsa.

Kwana uku kafin rasuwarsa, Sam ya halarci taron zaben ‘yan jaridu na Nijeriya (NPAN), a Legas. Ta hanyar wasu suka samu manyan mukamai biyu- shugaban da sakatare-janar, wadanda ake tunanin sun fito ne daga wani yanki na wannan kasa. Wasu daga membobin, ba su ji dadi da faruwar hakan ba, inda suka dage kan cewa; dole ne sai an canza. Amma Sam ya ki amincewa da wannan shawara, inda ya dage cewa; dole ne a kiyaye tare da yin adalci.

Duk da cewa, ba shi ne ya samu nasara ba, amma ya bukaci a yi abin da ya dace, ta hanyar yin adalci, ya kara da cewa; idan ba a yi adalci ba, a shirya ganin abin da zai biyo baya. A nan, ba don kansa yake yin fadan ba, yana yi ne domin wasu. Sam ya tsani zalunci a dukkanin abubuwan da ke tattare da shi. A karshe, dai adalci da gaskiya sun yi galaba bayan shiga tsakani da ya yi. Wannan jigon, jim kadan kafin mutuwarsa, ya kunshi sadaukarwarsa na tsawon rayuwarsa na gaskiya da adalci.

Sam bai gamsu da zama a matsayin dan kallo kawai ba. Ya yi kokari ya sa duniya ta zama wani wuri mafi kyawu da kyakkyawar dabi’a. Har ila yau, yana da hangen nesa na musamman, karfin hali da kuma juriya ta ban mamaki. Kamfanonin da ya kafa, sun tabbatar da imaninsa ga neman gaskiya, mutunci da kyakkyawar manufa.

A karo na farko da na yi aiki da shi shi ne, a ‘North Links Industries’ da ke Kaduna a shekarar 1993. Daga nan ne muka je Oakhouse Forte a shekarar 1997, daga nan kuma muka kafa Jaridar LEADERSHIP a shekarar 2004.

A LEADERSHIP, ni ne farko kuma tilo manajan da ke kula da albarkatunta. Sam ya nuna kishinsa da soyayya a lokacin da ya ba ni mukamin mataimakin babban manajan kamfanin na farko a tarihin kamfanin, bayan na gyara matsalar da ta kusan kashe kamfanin na makudan kudade. Daga baya kuma na zama babban manaja na farko a watan Yunin shekarar 2006, inda na ba da sanarwar wasu jerin matsayi na baya da suka sa na tashi zuwa manajan darakta na kamfanin LEADERSHIP, a watan Janairun 2011.

Zan iya tuna tafiye-tafiye da dama da na yi tare da shi a fadin Nijeriya. Sannan babu ko daya ya kasance na kasuwanci; illa kokarin hada ni da manyan mutane da yawon bude ido da sanin makamar aiki da kuma samun damammaki.

Mahaifiyarmu, ba ta amince Sam ya shiga siyasa ba. Sakamakon jin tsoron wani abu da zai iya faruwa da danta, musamman idan aka yi la’akari da rudanin da ke tattare da siyasar Nijeriya. Don haka, abu na gaba da ta yi da ya girgiza shi shi ne, yadda ta yi tattaki zuwa har inda yake; ta gan shi, da ta tabbatar sai ta yi masa addu’a. Ta yi addu’ar cewa;, “In sha Allahu za a yi lafiya, ba tare da wata matsala ko kunci ba.” Daga baya, suka ci gaba da magana har zuwa wayewar gari.

Lokacin da Sam ya rasu, fada wa mahaifiyarmu rasuwarsa; ba karamin tashin hankali ba ne. Ba na nan a lokacin, amma da na gan ta bayan wasu ’yan sa’o’i, sai ta yi ajiyar zuciya sosai ta ce; “Abin da ya faru ke nan? Me ya sa kuka bar shi ya mutu? Babu shakka, kalamanta sun yi matukar ratsa zuciyata. Ba komai ba ne kula, illa kukan bacin rai daga uwa wacce a koda-yaushe take yin addu’ar neman tsira ga ‘ya’yanta, sannan kuma ta yi imanin cewa; addu’arta na da matukar karfi.

Har ila yau, labarin Sam yana kuma dauke da sa hannun bangaskiyarta, kaunarta da bakin cikinta, akwai tunatarwa cewa; babu wanda ke samun girma gaba-daya da kansa, kazalika a bayan kowane babban mutum; akwai dangi wadanda ke daukar nauyin wannan girma.

Rayuwar Sam na dauke da addu’a mai zaburarwa: “Saboda haka, mun koyi kidaya kwanakinmu, domin mu bi zukatanmu ga hikima.” (Zabura 90:12). A wurinsa, wannan ba waka ba ce, sai dai salon rayuwa. Ya koya tare da sanin muhimmancin fitowar rana da manufar duk abin da ke kewaye da ita. Yana fara yin abin da zai yi, ba tare da jiran cewa sai gobe ba. Gaggawarsa ta kasance cikin hikima.

Rayuwarsa akwai albarka a cikin da babu asara a ciki. Gadon Sam daya ne, manufa, mutunci da kuma kauna. Bai taba kwanakin da yake da su ba. Ya cika su da ma’ana, ya bar hikimar da ta rayu bayansa. Har yanzu, sunansa yana bude kofa, kwakwalwa na karfafa zukata, sannan kuma misalinsa yana haskaka hanyoyi.

Rayuwar Sam na kunshe da jarumtaka da ra’ayoyi masu ban sha’awa. Ya kasance ma’aikacin hada-hadar magunguna, amma ya yi karfin hali ya kutsa zuwa kafofin watsa labarai, hanya mai hadari da ya bi bayan mahaifinmu Clement.

Shirye-shiryensa na kafofin watsa labaru, sun kasance wuraren tattaunawa na kasa, yin lissafi da hangen nesa. Yana da ma’aunai masu girma, karfin kuzari da tunani wadanda da kyar kowa ya mallaka. Ya kasance mai tsayin daka da karamci ga abokai da ma’aikatansa. Kirista ne shi mai ibada. Ba shi da tsoro, kuma ya kira abubuwa da sunayen da suka dace.

Shekara biyar bayan mutuwarsa, abubuwan alhairin da Sam ya bari suna nan. Ba ma makoki a matsayin wadanda ba su da wata makama. A maimakon haka, muna murna da albarkar tunawa da shi. Hangensa yana nan muna amfanarsa a duk lokacin da muka motsa shi da lokacin da muka bi ka’idojin da ya kafa da kuma duk lokacin da muka fayyace gaskiya. Har wa yau, sunansa ya ki bacewa. Abin alfahari ne, domin ya shuka Iri wanda ke ci gaba da ba da ’ya’ya. Ayyukansa suna biye da shi, kuma kwakwalwarsa tana da albarka.

Sam Nda-Isaiah, mutum ne mai tsananin hikima, jarumtaka da kuma nuna. Ya rayu cikakke, ya yi jagoranci, yana kuma yi kyauta ta yabawa. Kwanakinsa sun yi tasiri matuka, ta hanyar shahararren shafinsa a baya na, “Last Word”, ya bar gadon adalci da gaskiya a tsarin mulkin Nijeriya. Rubuce-rubucensa, sun tabbatar da ka’idojin da ke tabbatar da rashin son kai da adalci ga kowa da kowa da kuma tsarin da ake mutunta hakkin kowa. Suna kuma bayar da damar bude damammaki ga kowa da kowa, ba tare da la’akari da asalinsu ko halayensu ba.

Ka huta lafiya dan’uwa. Hakika zuciyarka ta kasance a kan hikima. Rayuwarka fitila ce ta adalci. Ina tsammanin ku sau da yawa a matsayin tushen karfi. Bayan shekaru biyar, muna bikinku, ba don abin da muka rasa ba, sai don rayuwar da kuka yi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace
Rahotonni

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda
Rahotonni

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

December 19, 2025
Sojojin somaliya
Manyan Labarai

Me Ke Kawo Yawaitar Juyin Mulki A Nahiyar Afirka?

December 14, 2025
Next Post
Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

Tinubu Ya Nuna Kwarewa Da Gogewa A Sha’anin Mulkin Nijeriya – Bishir Dauda

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Shugaban Somaliya: Kara Fadada Bude Kofa Ga Kasashen Waje Da Sin Ke Yi Zai Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

Shugaban Somaliya: Kara Fadada Bude Kofa Ga Kasashen Waje Da Sin Ke Yi Zai Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.