ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ke Kawo Yawaitar Juyin Mulki A Nahiyar Afirka?

by Sulaiman
9 months ago
Sojojin somaliya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Juyin mulki, wani lamari ne da ya zama abun mamaki a shekarun baya amma a ‘yan shekarun nan, a iya cewa, ba abun mamaki ba ne domin ya zama tamkar ruwan dare musamman a Nahiyar Afirka. 
Masoynmu masu bibiyarmu, me zai hana, mu tambayi kanmu, shin me ake nufi da juyin mulki kuma me ke kawo shi?
Juyin mulki, shi ne ƙwace gwamnatin ƙasa ba zato ba tsammani kuma ba bisa ƙa’ida ba, wanda yawanci sojoji ko ƙungiya mai ƙarfi ke yi, ta hanyar amfani da ƙarfi ko barazana domin cire zaɓaɓɓun shugabanni.
A wannan makon, alƙalaminmu zai karkata ne kan sharhi ga wannan muhimmin abu da ke barazana ga wanzuwar dimokuraɗiyya a yankin Afirka, duk da cewa, akwai dalilai masu ƙarfi da ke janyo a yi juyin mulki a ƙasa.
Ga bayani a sarari kuma a taƙaice game da manyan dalilan da ake kyautata zaton su suke haifar da juyin mulkin da ake yi kwanan nan a Afirka, musamman daga ƙarshen shekarun 2020 zuwa 2025.
Duk da cewa, kowacce ƙasa da na ta irin sanadin, kamar a ƙasashe irin Mali, Burkina Faso, Guinea, Nijar, Gabon, Chad, da Sudan da suka fada hannun mulkin sojoji a ‘yan shekarun da suka gabata.
Babban dalilin juyin mulki, bai gaza rashin Shugabanci na gari da cin hanci da rashawa. Gwamnatoci da yawa a ƙasashen da abin ya shafa suna fama da cin hanci da rashawa, rashin kula da ababen more rayuwar jama’a, rashin samar da wutar lantarki, ayyukan yi, ilimi, da kiwon lafiya na gari.
Wannan yana raunana amincewar mutane ga gwamnatocin farar hula kuma yana haifar da gurɓacewar mulkin dimokuraɗiyya wanda hakan ke bai wa sojoji uzurin karɓar mulki cikin sauƙi.
Wasu daga cikin dalilan sun haɗa da rashin tsaro da yawaitar tashe-tashen hankula. Ƙasashen Sahel, kamar Mali, Burkina Faso, Nijar – sun fuskanci hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi (IS, Al-Qaeda, JANIM), wanda hakan ya haifar da zargin cewa, jami’an tsaron ƙasa sun gaza. A duk lokacin da gwamnatoci suka gaza kare ‘yan ƙasa, sojoji sukan amfani da wannan dama wajen ƙwace mulki da nufin “dawo da tsaro.”
Wasu shugabanni, sukan yi yunƙurin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki don sauya kujerar dimokuraɗiyya ta zama ta dindindin, kuma su yi riƙa tafka maguɗi a yayin zaɓe, kamar Guinea (2021) da Gabon (2023). Wannan sau da yawa ya kan fusata jama’a sai hakan ya zama wani uzuri ga sojoji wajen hamɓarar da gwamnatin.
Har ila yau, wasu jama’a saboda fusata da salon mulkin dimokuraɗiyya a ƙasarsu, suna ganin sojoji a matsayin masu ceto, sun yi imanin cewa, sojoji za su kawo musu kwanciyar hankali. Wannan amincewar ta jama’a, yana sa juyin mulki ya yi nasara cikin sauƙi.
Jerin juyin mulki da aka yi cikin nasara a Afirka.
1 – Sojojin Mali a 2020 sun tsige Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta saboda rashin tsaro da zanga-zanga.
2 – Sojojin Chad a 2021 sun karɓi mulki a ƙarƙashin ɗan Shugaba Idriss Déby, bayan mutuwar sa.
3 – Sojojin Guinea a 2021 sun tsige Alpha Condé a 2021 bayan yunƙurin tsawaita mulkinsa.
4 – Sojojin Sudan sun rushe gwamnatin raba iko a 2021
5 – Sojojin Burkina Faso a 2022 sun tsige Shugaba Kaboré saboda gazawar dakatar da rashin tsaro. A juyin mulki na biyu kuma, wata tawagar sojoji ta hambarar da Laftanar Kanar Damiba duk a wannan shekara.
6 – Sojojin Nijar a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum.
7 – Sojojin Gabon a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo.
8 – Sojojin Guinea-Bissau a watan Nuwamban 2025, sun hamɓarar da gwamnatin Umar Sissoco Embalò.
Akwai jerin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa amma bai yi nasara ba da dama duk a nahiyar ta Afirka.
Juyin mulki
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Wacce Kasa Ce Za Ta Lashe Gasar Kofin Afirka

Yadda Haaland Ya Zura Kwallaye 100 A Firimiyar Ingila

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.