Tunisiya Na Da Masu Korona 922- Ma’aikatar Lafiya

A laboratory operator wearing protective gears runs tests on sample possibly infected with Covid-19 at the Henri Mondor Hospital in Creteil, near Paris, on March 6, 2020 as the novel coronavirus strain that erupted in China this year and causes the COVID-19 disease already left nine dead in France and made hundreds ill. - (Photo by Thomas SAMSON / AFP)

Ma’aikatar lafiya ta kasar Tunusiya, a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa an sake samun mutum hudu da cutar Korona a kasar, wanda wannan adadin ya kai mutum 922 da suke da cutar a kasar.

“Cikin mutum 438 da aka yiwa gwaji, an samu mutum 34 da suke da cutar a cikinsu, inda hudu ne sabbin masu cutar, a yayin da 30 kuma tun a gwajin baya aka tabbatar.” Inji sanarwar ma’aikatar lafiya.

Ya zuwa yanzu a kasar Tunusiya mutum 194 ne suka warke daga cutar, a yayin da 38 suka mutu daga cutar kamar yadda sanarwar ta tabbatar. Sanarwar ta ce wadanda yanzu ke samun kulawa a asibiti sun kai 110, inda 20 daga cikinsu ke cikin matsanancin hali.

A cewar sanarwar hukumomin, sun tabbatar da cewa zuwa yanzu an yi wa mutum 19,849 gwaji tun daga ranar 2 ga watan Maris zuwa yau a Tunusiya din.

 

Exit mobile version