Wani mahaifi mai shekaru 60 mai suna Malam Danjuma da ɗansa Ibrahim Danjuma mai shekaru 35 da kuma Aminu Gaye mai shekaru 35 sun rasa rayukansu yayin ciro wata waya da ta fada masai a kauyen ‘Yar Gwanda da ke karamar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewar mutanen uku sun makale ne a cikin ramin wata masai yayin da suke kokarin dauko wayar da ta fada ciki a ranar Lahadi.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara
- Tsaro: Nijeriya Za Ta Karbo Jiragen Yaki 24 Daga Kasar Italiya
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar wa LEADERSHIP faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya ce an ceto Alasan da ransa, yayin da sauran ukun kuma aka ceto su a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu a wani asibiti da ke Bichi.
A cewar Abdullahi, a ranar Lahadi 21 ga watan Afrilu, 2024, hukumar ta samu kiran agaji da misalin karfe 11:00 na safe daga wani Aminu Yar Gwanda, wanda ya sanar da faruwar lamarin.
Ya ce a lokacin da suka isa wajen, sun tarar da wani Malam Danjuma, mai shekaru 60 ya shiga cikin ramin domin ya ciro wayarsa da ta fada ciki amma ya kasa fitowa.
Ɗansa Ibrahim Danjuma mai shekaru 35, shi ma ya shiga ramin da nufin ceto mahaifinsa amma dukkaninsu suka makale.
Abdullahi, ya kara da cewa mutum na uku, Aminu T Gaye mai shekaru 35, wanda ya yi kokarin ceto su amma ya kasa, kazalika mutum na hudu Abbas Alasan mai shekaru 28 shi ma ya kasa ceto su.
Amma ya ce mutane uku da aka ceto an mika su ga jami’in ‘yansanda na shiyyar Tsanyawa.
Jami’in dan sandan da ya garzaya da su asibiti a Bichi, SP Iro Lado, ya tabbatar da mutuwar mutanen ukun, amma ya ce mutum na hudun na raye.