Umurnin Shugaban Ƙasa A Kan Sauƙaƙa Hada-Hada: Bincike Ya Nuna Huku-mar NIS Ta Ciri Tuta

Daga Bello Hamza

Wata uku da fitar da dokar tsaftatce filayen jiragen saman ƙasar nan domin sauƙaƙa hada-hada da gwamnatin tarayya ta  ba dukkanin Hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkokin jiragen sama, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) wadda ake ce wa ‘Imagirashin’ ta yi wa sauran Hukumomin zarra wajen gudanar da ayyukanta cikin lokaci a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Hukumar ta nuna cewa, ita jakada ce tagari a ƙoƙarin shigar masu zuba jari cikin ƙasar nan ba tare da ta naƙasa dokokin aiki ba, tare da tabbatar da tsaro da kuma binciken ƙwaƙwaf ga masu shiga da fita cikin ƙasar nan.

Ƙarƙashi jagorancin haziƙin shugaba Muhammad Babandede (MFR), jamia’an Hukumar Imagireshin sun yi aikin ganin masu zuba jari na gaskiya fiye da 20,000 suka shigo ƙasar nan ta hanyar ba su izinin shigo wa a lokacin shigowarsu ƙasar nan kamar yadda dokar ta tanada.

Hakan da bai samu ba a tsohon tsari wanda ya amince  da waɗanda suka karɓi izini a ƙasashen su ne kawai za su iya shigo wa ƙasar nan, abin da kan dagula ƙoƙarin masu zuba jari a cikin ƙasar nan.

Fara aiki da wannan doka a watan Yuni ya ɗora babban nauyi a kan sashin rundunar da ke filin jirgin sama na Legas, jami’an Hukumar kuma sun ba mara ɗa kunya ta hanyar gudanar da aikinsu yadda ya kamata, kuma yadda ake yi a saura ƙasashen da suka ci gaba, ba kamar yadda dokar ta samu sauran Hukumomi da ke aiki a filin jirgin saman suka gafala ba, a lokacin da gwamnati ta shigo da dokar. Hukumar tuni ta zabura ta kama aiki tun daga lokacin da ofishin shugaban ƙasa ya ba da umarnin aiki da sabuwar dokar.

Wani ɓangare na dokar ya tanadi cewa, duk wani jami’i da ya karɓi cin-hanci a wajen masu mua’amala da filayen jirgin zai fuskanci horo mai tsanani kuma za a kore shi daga aiki. Kyakyawan shugabancin da Hukumar ke da shi ƙarƙashin jagorancin Muhammad Babandede (MFR) ya sa jami’anta ba su samu matsala ba wajen gudanar da ayyukansu ƙarƙashi wannan sabuwar dokar ba.

Dama can Hukumar Filin jirgin sama ta Murtala Muhammad ta kafa doka cewa dole kowanne jami’i da ke aiki a nan ya riƙa fitowa cikin kyakyawan unifam tare da manna sunansa a jikin rigarsa,  hakan na sa a samu sauƙi wajen gane jami’an da mutun ke hurɗa da su.

Waɗannan dokoki ba su jami’an Hukumar wahala ba saboda tuni ta zaburar da jamia’anta wajen yin aiki yadda ya kamata kamar dai yadda aka tanada tsarin aikace-aikacen harkokin filayen jirage na duniya, a kan haka an shiryawa jami’ai kwasakwasai da tarukan ƙara ilimi da canza wa jami’ai wuraren ayyuka. Saboda haka koda dokar ta zo “bai zama wata matsala ba ga jami’anmu”

Binciken da Wakilinmu ya yi ya nuna cewa, baƙi na karɓar izinin shigo wa ƙasar nan, nan take a dukkan ɓangarorin filin jirgin saman, ba tare da ɓata lokaci ba, kuma daga watan Yuni da aka kafa dokar an ba da izinin shigowa ƙasar nan sama da dubu 20,000. Hakan ya sa baƙi sun gwammace su shigo kai tsaye su nemi izinin a filin jirgin sama maimakon karɓa a ofishin jakadanci na ƙasar nan a ƙasashensu. Binciken ya kuma gano cewa, dukkan jami’ai da ke aiki waɗannan wurare suna maƙale sunansu a ƙirjinsu domin baƙin su san wane ne suke hurɗa da su.

Wata majiya a filin jirgin saman ta bayyana wa wakilinmu cewa, shugaban Hukumar Imagireshin ne ya ba da umarnin dukkan jami’ansu su tabbatar suna liƙe da sunansu a ƙirji musamman waɗanda suke hulɗa kai tsaye da fasinjoji masu shigo wa daga ƙasashen waje, yin haka zai bada ikon gano duk wani jami’i da ya nemi na goro a hannun fasinja a kuma samu sauƙin horar da shi.

“wannan lamari ne mai mahimmanci sosai domin zai yi maganin ɓata-gari cikin jami’an da ake da su” in ji majiyar.

Daidai lokacin da wasu Hukumomi ke neman bakin zaren a kan yadda za su aiwatar da wannan doka tuni kamfanonin jiragen sama da fasinjoji ke yabo da Allah-san-barka ga Hukumar ta Imagireshin kan yadda suke aiwatar da wannan dokar. Musamman masu kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje, suna masu bayyana cewa, Hukumar ta cacanci yabo wajen ƙoƙarinsu na bada izini ga masu shigowa daga ƙashen duniya nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba, “hakan ya rage mana ƙarin nauyi da rashin yi haka kan jawo mana lokutan baya” in ji wani da ya buƙaci mu sakaya sunansa.

Masu jiragen na ƙasashen waje sun kuma bayyana cewa, a halin yanzu ma fasinjoji sun natsu da gamsuwa da irin aikace-aikacen jami’an Hukumar yadda suke aiki cikin fara’a da walwala yayin da suke gabatar da aikinsu.

Haka kuma, Hukumar Hana Fataucin Mutane (NAPTIP) ta nuna gamsuwa da haɗin kan da suke samu a yayin aiki da jami’an Hukumar Imagireshin a filin Jirgin Sama na Legas musamman wajen ganin an kawar da masu fataucin mutane daga filin jiragen ƙasarmu.

Da yake ƙarin haske ga Wakilinmu, wani jami’in NAPTIP wanda ya buƙaci mu sakaya sunansa ya nuna jin daɗinsa kan aiki tare da haɗin kan da suke samu daga jami’a Hukumar ba kamar da ba, ya kuma ƙara da cewa, “duk da ba mu da ma’aikata na din-din-din, jami’an Hukumar na sanar da mu a kan lokaci da zarar an kama wani da zargin fataucin mutane” in ji shi.

“A lokutan baya mukan ɓata ɗan kuɗaɗen da ke hannumu waje zirga-zirga zuwa filin jirgin sama domin samun labarin ko an kama masu fataucin mutane amma yanzu Hukumar Imagirashin ta sauƙaƙa mana wannan” in ji shi.

Bisa sabon tsarin da aka samar a halin yanzu na mallakar kati, fasinjojin da za su shigo ƙasar nan ko waɗanda za su fita, ba buƙatar sai sun cike fom ɗin Hukamar Kwastam.

Jami’an da ke bakin aiki, wanda suke bayar da izini shigowa ko hana shigo wa wannan ƙasa bayan sun duba kayan da fasinja ya shigo da su da kuma dalilin shigowarsa, ba a ba baƙin izinin shigo wa ƙasa har sai an tabbatar da sahihancin izinin shigowarsu kamar yadda dokar Hukumar ta shimfiɗa.

Wani ɗan ƙasar Kanada Todd Guozd, ya bayyana cewa, da bai zo Nigeriya ya ga ci gaban da aka samu ba wajen samun izini shiga ko fita ƙasar ba, ba zai taɓa yarda da cewa za iya samun izinin cikin sauƙi ba.

“Na ziyarci Nijeriya lokacin da na fara kasuwanci, a makon da ya wuce (lokacin da aka tattauna das hi). Tun daga irin abubuwan da na karanta na kuma ji marasa kyau a kan Imagireshin ɗin Nijeriya a wasu kafafen watsa labarai na duniya, ina tabbatar muku da cewa, da na shigo ƙasar sai na samu duk abin ba haka yake ba”.

“Lokacin da na sauka a filin jrgin sama, na gamu da wani jami’in Hukumar mai fara’a wanda ke bakin aiki. Na cika dukkan sharuɗɗan da Hukumar ta gindaya na samun izinin ta intanet, ba buƙatar sai na je ofishin Hukumar da ke Ottawa, Ontario. Saboda haka, cikin ƙaramin lokaci na samu izinin shiga ƙasar, kuma ko da na shiga ban samu wata matsala ba. Ina shiga na samu biza(takardar izini) ba tare da wahala ba, kuma na fahimci mutane da yawa na samun bizar ta su da zarar sun shiga cikin ƙasar, saboda wannan kyakkyawan labari ne da zan koma gida da shi. Na tabbatar da an samu ci gaba a Nijeriya a ɓangaren Imagireshin”, in ji ɗan ƙasar Kanadan. Kamar yadda baƙi daga ƙasashen waje ke yaba wa aikin an Hukumar Imagireshin haka ma fasinjo a filin jirgin saman da ke Legas ke yin irin wannan yabo wanda suke cewa lallai iƙirarin da gwamnati ke yi na canji, an fara samun sa a Hukumar ta Imagirashin, saboda wannan ke nuna an fara samun ci gaban da ake buƙatar samu a cikn ƙasa. Saboda fatan da al’umma ke yi shi ne dukkan sauran ɓangarori su ma a samu irin wannan sauyi a gurinsu.

Alhazan Nijeriya da suka dawo daga aikin hajin bana sun ce an samu gagarumin canji a Hukumar Imagirashin ganin yadda aka sauƙaƙa wasu wahalhalu da aka dinga fama da su a baya tsakanin fasinsijoji da jami’an Hukumar, ɗaya daga cikin irin waɗannan alhazan Alhaji Abdulraaf, wanda ya ce ya je aikin Haji sama da sau uku, sannan kuma ya yi zirga-zirga zuwa ƙasashen waje, inda ya nuna cewa an samu canji gagarumi wajen tafiyar ta harkokin Hukmar Imagireshin a filin jirgin sama na Legas.

Shi ma Jimoh, wanda ya daɗe yana hulɗa da Imagireshoin lokacin zirga-zirgarsa zuwa ƙasashen waje ya ce, “hulɗar da yake da jami’an a halin yanzu ta sha bamban nesa ba kusa ba da wancan lokacin, domin kuwa a wannan lokaci jami’an sun zama kamar basu ba saboda samun ƙwararren shugaba wanda ya ɗora su a kan hanyar aikin da ya kamata su yi daidai da dokar da ta kafa su.

Da yake an ce mutum tara yake bai cika goma ba, duk dairin wannan yabon da Hukumar ke samu daga abokan hulɗarta, sai dai akwai wani hanzari ba gudu, wanda Hukumar kula da filayen jirgin sama ta ƙasa ta Ankarar da Hukumar Imagireshin ɗin cewa, ta ƙara ƙaimi waajen tabbatar da cewa, ta kakkaɓe dukkan ɓata-garin jam’anta ta yadda za a ƙara samun ci gaba a Hukumar fiye da yadda ake tsammani.

Saboda haka idan ana buƙatar samun irin wannan cikakkiyar nasara sai dukkan jami’an da ke gudanar da aiki a filin jirgin sama, waɗanda suka ƙunshi, Hukumar da ke kula da lafiyar dabbobi ta ƙasa (NAƘS) da Hukumar Kwastam (NCS) Hukumar kula da lafiya a bakin gaɓa (PHS) da Jami’an tsaron da ke kula da filin jirgi sama (AƁSEC) da Hukumar kula da filin girgin sama ta ƙasa (FAAN)  sai sun haɗa kai sun taimaki juna.

Exit mobile version