Daraktan Gidajen Rediyon Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Ndace, ya bayyana cewa an kammala shirin fara watsa shirye-shirye da harshen Mandarin, wanda shi ne harshe a hukumance na ƙasar China. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai tare da tawagar VON ga Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai.
Ndace ya ce ƙara harshen Mandarin zai kawo yawan harsunan da VON ke amfani da su zuwa tara. A yanzu, hukumar na watsa shirye-shirye da Hausa, Igbo, Yarbanci, Fulfude, Turanci, Faransanci, Larabci da Swahili. Ya bayyana cewa dukkan kayan aiki da tsare-tsare sun kammala don fara aikin, da nufin tabbatar da ɗorewar wannan sabon shiri.
- China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 11, Sun Rusa Sansanoni A Dajin Sambisa
A cewarsa, wannan shiri ya yi daidai da hangen nesa na shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ke fatan inganta dangantaka da China. Ya ƙara da cewa hakan zai tallafa wajen yaɗa sahihan labarai game da Nijeriya da China a duniya, tare da ƙarfafa musayar shirye-shirye da tunani tsakanin ƙasashen biyu.
Jakadan China, Yu Dunhai, ya ce wannan mataki zai zurfafa haɗin gwuiwar kafafen watsa labarai tsakanin ƙasashen biyu, bisa yarjejeniyar da aka cimma lokacin ziyarar shugaban Nijeriya zuwa China. Ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a dangantakar diflomasiyya da zai ƙarfafa musayar al’adu da fahimtar juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp