Tun bayan bullar wani faifan bidiyo da ke nuna wasu sojojin Nijeriya na yin sulhu da ‘yan bindiga a wani kauye mai suna Fankama da ke karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina jama’a da dama ke tambayar wane ne ya yi zaman sulhu da ‘yan ta’adda?
A cikin faifan bidiyon, an ji wani mai magana da ba a nuno fuskarsa ba, yana bai wa wasu mutanen umarnin cewa ga ‘yan bindiga nan za su zo su wuce, kar wanda ya ce musu komai.
Ga abin da yake cewa, “Hello, Sunusi, don Allah ina son, kana ji? Ka biyo bakin hanya duka ka gaya ma mutane cewa, don Allah ga Fulani nan za su zo su wuce, ba ruwan kowa da su (an yi sasanci), an yi magana ne yanzu za su zo, wucewa kawai za su yi, ka gane, a bi bakin hanyar nan kar wanda ya ce wani abu, ga su nan wucewa kawai za su yi, don Allah a bi ga su nan za su taho yanzu don Allah, a bi a gaya wa mutane, eh, yauwa.”
Hakazalika, a wani bidiyon an ji wani daga cikin Fulanin da ake sulhun da su yana neman a bayyana sunayen wasu talakawa da aka yi garkuwa da su a yankin Dandume da Sabuwa da kewaye domin su je su bincika a sako su, kana ya ce Fulanin “suna korafi a kan kasuwanni da hanyoyin da za su rika bi suna lalurorinsu, wani tabbaci za a ba su?”.
Daga can sai aka ji muryar wani jami’in sulhun yana cewa, Fulanin su fada musu hanyoyin da suke son bi su yi huldodinsu na yau da kullum tare da ba su tabbacin babu wani abin da za a yi musu. Yayin da shi kuma daya daga cikin jagororin ‘yan bindigar ya kada baki ya ce, “to yanzu kana ji? Mu yanzu hanyoyinmu ba bari muna shiga gari ta nan, shiru ne kawai, hai dai mutum ya kama wuri ya zauna, don wannan da ake ce wa Ali da ya ga mutum ya kama shi, ya wuce da shi kenan. Inda muke zuwa gari ba hanya. Mu kawai a daji muke, ba ka ganin yanayinmu? Ko ba haka nan ba? Abincinmu shi ne ‘ya`yan itatuwa, dubi wannan yadda ya rame (yana mai nuna wani a cikin Fulanin.”
Daga nan ne wani babban jami’in soja da ke wurin ya amsa da cewa, “Kar ka damu, in dai Aliyu ne, ni zan mai magana, in dai ka yi mun alkawari komai lafiya ne. Ka ga yanzu bari na fada maka gaskiyar lamari. Kwanakin baya kun kashe mun officer na a nan Unguwar Rimi, Sabuwal Local Gobernment. Unguwar Rimi idan ka wuce Maigora. Yanzu sai ya fada mana matsalar da ke damunsa mu ma mu fadi namu, daga nan sai mu sami matsaya a daidaita.”
Ana cikin haka ne kuma sai wani ya mike a wurin zaman sulhu da ya ce su wakilai ne daga Abuja, ya fara magana kamar haka, “Jama’a assalamu alaikum. Sunana Muhammadu Awwal daga Abuja.. ni ina daga cikin wakilai wanda aka turo daga Abuja, bangaren ministoci da suka samu tattaunawa da jami’an tsaro da kuma wasu daga cikin manya na Gwamnatin Tarayya Abuja wanda da ni da Bello muka taso daga Abuja kuma muka zo muka samu sauran abokanan aikinmu daga yankin Gusau har ta kawo yau muka zo nan (Katsina). Kamar yadda Alhaji ya fada, wannan shi ne zama na uku. Mun yi zama a Bawo, mun yi zama a Bagega a Anka (shekaranjiya), wannan shi ne zama na uku kuma in sha Allahu ba za mu tsaya iya nan ba za mu ci gaba yi.
“Alal hakika mun taho da tabbaci na su mahukunta daga sama dangane da bukatar da aka yi a kan a ci gaba da zama a yi sulhu, tun da ana ta iya kokari a baya da sauransu kuma ana ganin yadda abubuwa suke tafiya, to aka ga aka ga yiwuwar daga bangaren kowa da kowa, daga su daga ku da mu gaba daya, aka ga cewa a rika zama ana tattaunawa kuma tattaunawar nan in sha Allahu bil-hakki aka zo da ita wanda akwai maganganu, zan yi wasu, sannan a cikin wasu maganganun da za su fito, Alhaji Bello zai yi magana. Daga bangarenku dai sako daga wajen Gwamnatin Tarayya shi ne suna masu nuna jin dadinsu da kuma yaba muku a kan amsa kira ko kuma nuna cewa a zo a yi wannan zama na sulhu kuma in sha Allahu abu ne na gaskiya da za a ci gaba da yi har a ga an cimma burin abin da aka saka a gaba in sha Allahu saboda kowa ya koma yana cikin harkokinsa.
“Amma akwai magana da Bello in ya tashi zai fadada shi wanda kuma gaskiya daga zaman da aka yi ko kuma wasu abubuwa da aka yi daga bangaren su kansu mahukunta a nan wurin duk ana ganin ci gaba. Amma magana ce guda uku wanda muke so su Alhaji, an fara daukar wannan alkawarin, a bangaren Alhaji mutanenka sun fara cikawa. Magana ta daukar mutane, magana ta tare hanya, magana ta kisa ko kuma ‘attacking’, ma’ana kai wa garuruwa hari, akwai bukatar a dakatar sannan kuma kamar yadda shi mai girma kwamandanmu na nan ya yi magana, za mu ji daga bakinku.. wanda mun yi imanin kowa shuwagabannin da ke nan, ko Alhaji ne yanzu misali, ya yi magana ya ce ya fadi korafinku ta zauna, tun da duk wani wanda zai yi magana karshenta ka ga wanda zai biyo baya zai maimaita abin da zai fada ne. Saboda haka kofa a bude take.. da fatan Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagora kan wannan al’amari.
“Kuma mun yi Imani tun da mai unguwa yana nan sauran dattijai suna nan duk abin da aka fada aka tattauna kuma za su je su wayar wa da jama’a mutanen gari kai ko da akwai wani abu a cikin zukatansu da suke zargi kun dai ji kuma a gabanku aka yi, yauwa, Allah ya shige mana gaba.” In ji shi.
Bayan haka ne sai daya daga cikin shugabannin ‘yan bindigar wanda hoton bidiyon ya nuna tabbas, Ado Aleiro ne da aka taba warware nadin da aka yi masa na Sarkin Fulani a Masarautar ‘Yan Doto, ya fara magana da cewa, “yanzun nan wannan zama da muke yi ya shafi kananan hukumomi ne guda uku,muna maganar Sabuwa, Dandume, Faskari.”
Kwatsam sai babban jami’in tsaron da ke wurin ya katse shi ya ce, “ina ga bari in dan gyara masa kadan, assalamu alaikum. Kamar yadda mai gabatarwa ya gabatar daga farko cewa wannan zaman da ake yi ba zama ne kawai abin da ya shafi ‘state’ guda daya ba, abu ne wanda ya shafi kasa gaba daya. Saboda me? Wakilai ne daga ko ina suka zo daga sassa daban-daban wanda yake wannan wakili ne babba, wakilai ne ma da aka turo daga Abuja don su zo su saurari me za a tattauna a kai. ‘So’ kuma ni da na zo da nake ‘representing’ fiye da ‘local gobernment’ guda uku, ba wai abin ya tsaya nan ba. Faskari, nan ne kamar ‘tactical headkuatres’ dinmu na Katsina gaba daya kuma shi babban kwamandanmu na Katsina gaba daya shi ya turo ni, duk abin da aka tattauna na gaya mashi to kamar an gaya ma mu gaba daya Katsina ne, to shi ne nake so in dan yi gyara a kai.” A nan ne bidiyon ya yanke
A yayin zaman dai, an ambaci hanyar Funtuwa zuwa Tsafe a matsayin wurin da aka bukaci ‘yan bindigar su gaggauta daina kai hare-hare.Kana cikin wadanda suka halarci zaman har da wani da ya yi kama sosai da Bello Turji.
Wannan lamari dai zama wani batu da ya ja hankali musamman a kafafen sada zumunta na zamani saboda irin yadda Gwamna Dikko Umar Radda ya sha alwashin ba zai taba zaman sulhu da ‘yan ta’adda ba.
Haka kuma faifan bidiyo ya fara dora shakku game da maganar Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya yi na cewa babu shi babu sulhu da ‘yan ta’adda kuma ya shirya tsaf domin kawar da su ko ta halin kaka.
Taron zaman sulhu an yi shi ne a cikin firamare ta garin Fankama kuma babu gayyatar wasu mutanen gari ko shuwagabannin al’umma, ga alama an yi wannan zaman ne tsakanin su jami’an tsaro da kuma yan bindiga bisa wata yarjejeniyar da ba a bayyana ba.
Batun ware kudi Naira biliyan 7.8 wata Alama ce da ke nuni da cewa gwamnan da gaske yake yi a kan batun samar da tsaro da ya hana Jihar Katsina yin rawar gaban hatsi.
Amma kuma batun wannan sulhu da ke yawo a kafar sadarwa ta intanet ya jefa shakku a zukatan al’umma, inda wasu ke cewa anya gwamnati da gaske ta yi a kan wannan al’amari?
Wata majiya daga bangaren Gwamnatin Jihar Katsina ta shaida mana cewa ana zargin wadannan jami’an tsaro sun zo ne karkashin umarnin karamin ministan tsaro Dakta Bello Matawallen Muradun domin yin wannan aiki na musamman.
A ranar Asabar da ta gabata ne al’ummomin wannan yanki na Fankama suka rika ganin bakin jami’an tsaron sojojin Nijeriya suna yi wannan gari kawanya tare da ‘yan bindiga da suka addabi Jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Kaduna da kuma Neja.
To sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’an tsaro ne suka yi nasarar yin wannan sulhu da ‘yan bindiga wadanda ke sace mutane suna kashewa ko kuma su dauke sai an biya kudin fansa da su daina wannan mummunar sana’a su rungumi zaman lafiya.
Majiyar Leadership Hausa ta ce daga cikin abubuwan da wannan sulhu ya cimmawa sun hada samarwa da ‘yan bindiga labi da aka maida gonaki da samar masu da makarantu da madatsun ruwa da kuma asibitoci.
Wani labari da ake ganin yana da alaka da wannan sulhu da Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ba ta san da shi ba shi ne, yadda aka ga ‘yan bindiga sun sako mutane 18 da suka yi garkuwa da su a ranar Litinin din da ta gabata.
Yanayin yadda wadannan ‘yan bindiga suka halarci wannan zaman sulhu da ba a ji dukkanin abubuwan da suka tattauna ba ya tada hankali musamman ganin ‘yadda suka tafiyar da lamurran su babu wata fargaba.
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina a ta bakin Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadik ya shaida wa Leadership Hausa cewa ba su da labarin zaman sulhu da aka ce an yi tsakanin wasu jami’an tsaro da kuma ‘yan bindiga.
Haka nan wata majiya ta ce, jami’an tsaro da shugaban wata kungiyar Fulani ta kasa ne suka yi sulhun da ake magana, sai dai ba a fadi katamaimen wane shugaba ba ne.
Bugu da kari majiyar ta ce, bayan an share wa ‘yan bindigar hanya, sun koma cikin dajin da suka fito ne, yayin da kuma mutanen garin na Fankama suka rika yin Allah wadai da lamarin musamman yadda ‘yan bindigar suka yi wa garinsu kawanya dauke da makamansu.
Sai dai a wani yanayi da za a kira da tsugune ba ta kare ba, bayan zancen sulhu da ‘yan bindigar ya mamaye gari, wasu ‘yan bindigar sun tare hanyar Sheme zuwa Kankara inda suka yi awon gaba da wasu mutane.
Majiyarmu ta ce dama ko da sulhun da aka yi da ‘yan bindigar ya tabbata, akwai wadanda ba za su hakura ba, domin sukan ce wadanda suka ajiye makamansu sun riga sun tara dukiya, su kuma da ba su da komai ba za su daina ba, lamarin da ke kara wa masu yunkurin sulhun cewa har yanzu da sauran rina a kaba.