Wa’adin da Shugaba Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya bai wa hukumomin tsaro na su karbo bashin Naira tirilayan 1.1, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba wa manoman shinkafa a karkashin shirin aikin noma na ‘Anchor Borrowers’, ya cika, amma shiru ka ke ji har yanzu wadannan manoma ba su maido kudaden ba.
Idan za a iya tunawa, Shugaba Tinubun ya umarci hukumomin su karbo wadannan zunzurutun kudade kafin ranar 18 ga watan Satumbar 2023 da muke ciki.
- Xi Ya Karfafawa ‘Ya‘yan Wadanda Suka Sadaukar Da Rayuwarsu Da Su Zama Amintattu Masu Kare JKS Da Al’umma
- Kaunar Da Xi Jinping Yake Nuna Wa Gari, Dangi Da Kuma Al’ummar Kasa
An bayar da wannan bashi ne domin kokarin sake habaka harkokin noma a Nijeriya tun a shekarar 2018. Koda-yake dai shirin ya samu nasarori a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, inda kuma ya samu tasgaro a wasu jihohin sakamakon kin biyan bashin da wasu daga cikin manoman shinkafar da suka amfana suka yi.
Kazalika, an yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an da aka dora wa nauyin bayar da bashin, sun karkatar da wani kaso daga cikin kudaden domin amfanin kawunansu.
Daga cikin wannnan adadi na Naira Tiriliyan 1.1 da aka bai wa Manoman Shinkafar, Naira biliyan 546 kacal aka iya maido wa. Amma, bisa wannan umarni da Shugaban Kasar ya bayar ne, ake sa ran manoman da suka ki biyan wadannan kudade da kuma sauran jami’an da aka dorawa nauyin karbo bashisshikan, suka karkatar da wani kaso daga ciki, za su maido da sama da Naira biliyan 577.
Bugu da kari, wannan ya hada daruruwan manoman shinkafar da suka yi rijista da kungiyoyi aka ba su wannan rance, da ya hada da kayan aikin noma kamar takin zamani, magungunan feshi da sauransu.
Ana sa ran kuma manoman za su biya bashin ta hanyar bayar da wani bangare na amfanin da suka girbe ko kuma ta hanyar biya da kudi lakadan.
Sai dai, karbo wannna bashi ya zamo wa Babban Bankin CBN wani babban kalubale ganin cewa, duk iya kokarin da aka yi na karbo bashin ta hanyar kungiyoyin manoman shinkafar, amma hakansu bai cimma ruwa ba.
Har ila yau, domin cika wannan umarni na Shugaba Tinubu, kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN), ta fitar da wata takarda mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Agustan 2023, inda ta umarci kafatanin rassan kungiyoyinta na jihohi da su yi aiki tare da jami’an tsaro domin karbo wannan bashi.
Sai dai, tun bayan wannan umarnin na RIFAN, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bashin da aka karbo daga gun manoman da suka amfana a jihohin, bai taka kara ya karya ba.
Haka zalika, dalilan da suka janyo tarnaki wajen karbo wadannan bashisshika, kamar yadda Mataimakin Sakatare Janar na RIFAN din reshen Jihar Kano, Malam Ado Hassan, ya shelanta suna da daman gaske.
Hassan ya kara da cewa, kungiyar reshen jihar ta karbi bashin na kimanin Naira biliyan 12 daga 2017 zuwa 2020, amma bashin da ta iya karbo wa daga wurin wadannan manoma da suka amfana, bai wuce kaso 30 a cikin 100.
Sannan ya yi ikirarin cewa, a kakar noma ta 2018 ‘ya’yan kungiyar reshen jihar, manoman shinkafa 44, 807 ne suka amfana a karkashin wannan shiri, duk kuwa da cewa sun fuskanci mummunar ambaliayar ruwan sama a wannan shekarar.
Ya ci gaba da cewa, a 2019 an fuskanci kalubalen Annobar Korona, wadda ba manoman shinkafa kadai ta shafa ba har da hada-hadar kasuwanci a fadin duniya baki-daya.
Sannan ya sake kokawa kan cewa, manoman shinkafar ba su samu wata diyya a kan asarar da suka yi ba, bayan afkuwar wannan annoba tare da kuma ta ambaliyar ruwan sama daga wurin Kamfanin Inshorar Aikin Noma na kasa (NAIC) ba.
Kazalika ya ce, a kungiyance an kai wannan rahoto kan afkuwar wannan annoba guda biyu, koda-yake an turo Jami’an CBN da na NAIC, zuwa gonakan manoman domin tantance asarar da suka tabka, amma shiru kake ji babu wani agaji ko tallafi da aka kawo musu.
Sannan sun bi hanyoyi da dama don karbo bashi, ciki har da yin amfani da sarakunan gargakiya, kotuna da sauran dabaru daban-daban, amma abin ya faskara.
Har ila yau, wani manomin shinkafa a Jihar Kano, Alhaji Ahmadu Usman ya yi nuni da cewa, zai wuya a iya karbo wadannan basussuka, domin kuwa ba hakikanin manoman da suka dace aka baiwa bashin ba, ‘yan siyasa aka bai wa suka yi san ransu.