Hussaini Yero" />

Wadanda  Suka Yi Garkuwa Da ‘Ya’yan Shugaban Jam’iyyar APC A Zamfara Sun Nemi Naira Milyan 50

Garkuwa

Wadanda su ka yi garkuwa da ‘ya’yan shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Maru, ta jihar Zamfara, Alhaji Sani Gyare Kadauri, sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan hamsin na yaran bakwai da suka sace a ranar Juma’a da ta gabata.

Wadanda suka sace sun hada da, Bashar da Abubakar da Haruna da Habibah da Sufyanu da Mubarak da Armayau da Masu garkuwa  sun sace su ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kauyen Kadauri.

Mahaifin yaran ya bayyana  wa manema Labarai ta waya cewa, Masu garkuwa sun kirashi sun gaya masa ya kawo kudin miliyan hamsin ko ya rasa ‘ya’yan nasa.

“Sun kira ni sun tambaye ni in biya niara miliyan N50m don sakin yarana su bakwai kuma sun yi gargadin cewa za su kashe su idan ba a biya kudin a kan lokaci ba,” in ji shi.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya tuntubi hukumomin da abin ya shafa kan batun, Gyare ya ce, “Babu bukatar inyi magana dasu  tunda suna sane da abin da ya faru da ni kuma ba wanda ya tausaya min.

“Hatta Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Bala Bello Maru, wanda ya fito daga Karamar hukuma ta, bai zo gidana don tausaya min ba, kuma bai kira ni a waya ba.”

Ya kuma koka kan yadda Shugaban Karamar hukumar, Alhaji Salisu Dangulbi, shi ma bai tuntube shi kan lamarin ba.

“Ina jin damuwa sosai;  Ina jin kamar ni cikakken bako ne kuma ban san abin da zan yi a wannan lokacin ba, saboda ba zan iya biyan kudin da wadannan mutane marasa zuciya suke nema ba, “inji Gyare.

Ya lura cewa ba zai iya tara kudin da Masu garkuwa suke nema ba ko da kuwa ya sayar da duk kadarorinsa, yana mai cewa, “Na yi masu bayanin hakan ne a kan wayar amma kawai sai suka yi min dariya.”

Gyare ya nuna rashin jin dadinsa game da halin rashin yarda da halin da hukumomin da abin ya shafa ke nunawa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

Ya ce ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da yaran nasa ba tare da turjiya daga jami’an tsaro ba, wadanda aka sanar da su abin da ke faruwa a kauyen.

A cewarsa, lokacin da Masu garkuwa suka shiga kauyen, an sanar da’ yan sanda amma ba su zo wurin ba sai bayan awa uku bayan sun gama aikinsu suka tafi.

Don haka, ya yi kira ga Gwamnatin  jihar da gwamnatin tarayya da su kawo agaji tare da kubutar da yaransa.

‘Yan jaridu suka  tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce yana sane da yaran da aka sace, amma ba shi da masaniyar kudin fansa na miliyan  N50m da  Masu garkuwa suka nema.

Exit mobile version