Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, ta zuba zunzurutun kudi kiminin Naira biliyan 309 a fannin aikin noma; domin samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Kyari, ya sanar da hakan ne; a matsayin guda daga cikin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a cikin shekara daya, wanda har ila yau kuma yake nuna nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a zangonsa na shekara daya.
- Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Kwalejin Noma Da Duba Aikin Babban Asibitin Maradun
- Sanata Saliu Ya Raba Taki Da Injinan Ban Ruwa Ga Manoman Kwara
Ya ce, kokarin da ake yi na samar da wadataccen abinci, musamman mai gina jiki, gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin noman rani; wanda aka noma Alkama a kadada 118,657 da suke a jihohin wannan kasa sha biyar, musamman don noman da zai dauki har tsawon zagayowar wata shekarar.
Ministan ya kara da cewa, gwamnatin ta kuma rabar da tan 58,500 na Shinkafa a daukacin jihohin wannan kasa, ciki har da Abuja da nufin karya farashinta tare kuma da rabar da sauran kayayyakin abinci masu dauke da sinadarin ‘Bitamin A’.
Kyari ya ci gaba da cewa, a kokkarin dakile hauhawar farashin kayan abinci, gwamnatin ta kuma rabar da tan 60,432 na ingantaccen Irin noma kimanin tan 887,255.
”Gwamnatin ta kuma rabar da buhunhunan takin gargajiya kimanin 62,328, da kuma kayan aikin noma ga manoma a wannan fannin na noma, domin samun riba tare da kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa baki-daya.
“Domin a samar da ingantaccen tsaro a gonakin manoma, an kara wa jami’an ‘yan sa kai da ke bayar da tsaro a wadannan gonaki na manoma, wato wadanda ake kira a turance ‘agro rangers’ da kuma sauran jami’an tsaron da ke aikin bayar da tsaro a gonakin kudade”, a cewar Kyari.
Kazalika Ministan ya bayyana cewa, gwamnati ta yi matukar kokari wajen bunkasa fannin kiwo da kula da lafiyar dabbobi tare kuma da kara karfafa gudanar da yin bincike a fannin kiwo da sauran ayyukan da suka shafi fannin kiwon.
Haka zalika a cewar tasa, gwamnati ta kara kaimi kwarai da gaske a wannan fanni na noma tare kuma da sarrafa Waken Soya, Kantu, Citta, Zobo da sauran kayayyakin amfanin gona, don a rika fitar da su kasashen waje ana sayarwa.