• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Waiwaye Game Da Yadda Kasar Sin Ta Tallafawa Duniya A Fanin Yaki Da Annobar COVID-19

by CMG Hausa
3 years ago

Tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasashen duniya sun dukafa wajen ganin bayan cutar, ta hanyar daukar matakai daban daban a lokuta mabanbanta, kuma matakin samar da alluran rigakafi masu inganci na sahun gaba a wannan muhimmin aiki.

Cikin kusan shekaru uku da suka gabata, kasar Sin ta yi rawar gani a fannin bincike da samar da rigakafin COVID-19, inda ta sauke nauyin dake wuyanta ta fuskar samar da rigakafi mai inganci ga alummun duniya baki daya.

  • Me Ya Sa Kasar Sin Ta Dinga Yaki Da Cutar COVID-19 Har Tsawon Shekaru Uku?

Cikin shekarar 2020, masu binciken kimiyya na kasar Sin sun kirkiro tare da gwada nauoin rigakafin wannan annoba daban daban, inda ya zuwa watan Mayun shekarar 2021 da ta gabata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ta sanya rigakafin Sinopharm cikin jerin rigakafin COVID-19 da aka amince a yi amfani da su a mataki na gaggawa. Rigakafin da ya zama na farko samfurin kasar Sin da WHO ta amince da shi, kuma na 6 a duniya da ya samu amincewar hukumar.

Daga bisani, kamfanin Sinovac ya sake fitar da karin rigakafin cutar ta COVID-19, wanda shi ma ya samu amincewar hukumar WHO domin amfani da shi a matakin gaggawa.

Idan an kwatanta da wasu nauo’in rigakafin cutar COVID-19 na kamfanonin Moderna da Pfizer, samfurin rigakafin kasar Sin na da fifito, kasancewar za a iya daukar sa daga wuri zuwa wuri cikin naurorin sanyaya abubuwa na amfanin yau da kullum, ba tare da sun lalace ba. Hakan na nufin rigakafin na Sin sun dace da yanayi irin na kasashe masu tasowa, wadanda ke da karancin wuraren adana rigakafi dake da bukatar wuraren ajiya masu sanyin gaske.

LABARAI MASU NASABA

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

A daya bangaren kuma, tun bayan da kasar Sin ta shiga shirin samar da daidaito wajen rarraba rigakafin annobar COVID-19 wato shirin COVAX” a watan Oktoban shekarar 2020, kasar ta ci gaba da mika kyautar rigakafin cutar ga sassa daban daban na duniya. A watan Agustan shekarar bara, Sin ta alkawarta ba da tallafin rigakafin COVID-19, wanda darajarsa ta kai dalar Amurka biliyan biyu ga kasashen duniya daban daban, tare da karin tallafin dala miliyan 100 ga shirin na COVAX.

Ya zuwa watan Mayun shekarar 2022, Sin ta samar da tallafin kayayyakin yaki da annobar ga kasashe 153, da hukumomin kasa da kasa masu nasaba da wannan aiki har 15.

Kasar Sin ta bayar da agajin rigakafin COVID-19 guda biliyan 2.2 ga kasashe daban daban. Kaza lika ta tura tawagogin kiwon lafiya zuwa kasashe 34, ta kuma rarraba kwarewar wannan muhimmin aiki na yakin da cutar tare da kasashen duniya sama da 180, da ma wasu hukumomin kasa da kasa, matakan da dukkaninsu suka yi matukar samun yabo daga daukacin sassan duniya, musamman ma kasashe masu tasowa wadanda su ne suka fi cin gajiya daga wadannan tallafi na Sin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Next Post
Shugabannin Nijeriya Da Nijar Za Su Bude Gasar Karatun Kur’ani A Zamfara Gobe Juma’a

Shugabannin Nijeriya Da Nijar Za Su Bude Gasar Karatun Kur'ani A Zamfara Gobe Juma'a

LABARAI MASU NASABA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.