‘Yansanda a Jihar Koros Ribas sun kama wani dan shekara 49 mai suna Eyo Etim, bisa zarginsa da kashe wata budurwa mai suna Harmony Edemawan a yankin Atim da ke karamar hukumar Akpabuyo.
An ruwaito cewa, wanda ake zargin an cafke shi ne a ranar bikin Kirisimeti.
- Liverpool Ta Sayi Cody Gakpo Daga PSV
- Masu Son Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magudi A Zaben Bauchi, Ba Za Su Yi Nasara Ba – Bala Mohammed
Wata majiya a karamar hukumar Akpabuyo, ta shaida wa LEADERSHIP cewa, asirinsa ya tonu ne lokacin da wasu ‘yan sintiri a yankin suka gudanar da bincike a gidansa bayan an samu labarin bacewar budurwar.
A lokacin bincike, ‘yan sintirin sun ga jini a kasa gidan inda suka gayyato ‘yansanda zuwa gidan, nan take ‘yansandan suka bayar da umarnin bude tankin ruwan, inda aka ga gawar budurwar a cikin tankin.
Budurwar dai, ta kasance ma’aikaciya ce a kamfanin Lafarge Holcim, inda kuma bayan gano gawarta, ‘yansandan suka kama Eyo Etim bisa zarginsa da kitsa kashe Edemawan saboda bashin da yake binta.
An ruwaito cewa, budurwar ta bace ne tun a ranar 22 ga watan Disamba, 2022.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Sule Balarabe, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, Eyo na hannunsu a yanzu.
Ya ce, Eyo ya basu bayanan karya na cewa, budurwar ta sayar da wata kadararsa da kudinta ya kai kimanin Naira miliyan tara sannan kuma taki biyansa.
Sule, ya kara da cewa, Eyo ya yi hayar wasu mutane su sace ta don ya karbi kudinsa, amma aka kashe ta aka kuma boye gawarta a cikin tankin ruwan, inda ya ce, ana ci gaba da bincike don a kamo sauran mutanen da hada baki da su don hallaka budurwar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ya ranci bashin budurwar har kimanin Naira miliyan 1.2 wacce kuma aka ce, yana yin soyayya da wata ‘yar uwarta mai suna Ruth Edem ‘yar shekara 22 kuma daliba a jami’ar UNICAL.
Wani dan uwan budurwar da bai bukaci a bayyana sunansa ba ya ce, Eyo ya ranci kudin budurwar kimanin Naira miliyan 1.2 a farkon wannan shekarar don bunkasa kasuwancinsa na sayar da manja.