Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Jamaica, wajen daidaita dabarun raya kasa, da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da inganta mu’amala tsakanin al’ummomi da musayar al’adu, da karfafa tushen ra’ayin jama’a, a wani mataki na sada zumunta tsakanin Sin da Jamaica.
Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da firaministan Jamaica Andrew Holness, ganawar da ta samu halartar ministocin harkokin waje, kudi, kiwon lafiya da kayayyakin more rayuwa na kasar Jamaica.
- Shugaban Kasar Tunisiya Ya Gana Da Wang Yi
- Wang Yi Ya Yaba Da Dankon Zumunci Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka
A jawabinsa Holness ya tunatar cewa, a shekarar 2009, ya samu damar tarbar shugaba Xi Jinping, wanda ya ziyarci kasar Jamaica a matsayin mataimakin shugaban kasar Sin, kuma a shekarar 2019, shi da shugaba Xi sun bayyana hadin gwiwa tare da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa manyan tsare-tsare.
Ya kuma bukaci Wang ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi, yana mai cewa, kasar Sin ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa kasar Jamaica yayin da ta fuskanci matsaloli, wanda ya taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Jamaica da inganta rayuwar jama’ar kasar, kuma ya nuna a fili cewa, kasar Sin na son taimakawa kasashe masu tasowa.
Firaministan ya jaddada cewa, Jamaica za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da ba da fifiko kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kokarin kulla kawance mai karfi bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Ibrahim)