Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce duk da cewa bangarori daban-daban ke iya samun sabani kan fahimtar dokokin duniya, fahimta ta bai daya ita ce daukaka tsarin dokokin duniya karkashin jagorancin MDD da ka’idojin huldar kasa da kasa bisa muradu da dokokin MDD.
Wang Yi ya bayyana haka ne jiya Juma’a, lokacin da yake amsa tambayoyi yayin wani taro mai taken “Kasar Sin a duniya”, wanda aka yi yayin taron tsaro na Munich dake gudana.
- Zaɓen Katsina: An Samu Ƙarancin Masu Kaɗa Ƙuri’a Da Zargin Sayen Ƙuri’u
- Benedict Peters: Gwarzon Dan Kasuwa 2024
Da yake amsa tambaya kan yadda za a shawo kan rikice-rikice da yanayi da tsarin duniya ke fuskanta, da yadda za a kaucewa nuna fuska biyu yayin aiwatar da dokokin duniya, Wang ya ce kasar Sin ta samu ci gaba karkashin wannan tsari na yanzu, kuma ta ci gajiyarsa.
Ya ce abun da ake bukata shi ne, inganta ci gaban wannan tsari bisa adalci da alkiblar da ta dace, ta yadda za su dace da muradun galibin kasashe.
A martaninsa game da huldar Sin da Amurka kuwa, ministan ya ce manufar Sin ta dogara ne kan ka’idoji 3 na mutunta juna da zaman lafiya da kuma hadin gwiwar moriyar juna.
Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci.
Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan Sin da Amurka. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)