A yau Talata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaran aikinsa na Rasha Sergey Lavrov, suka gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Beijing.
Yayin da yake amsa wasu tambayoyi, Wang Yi ya yi karin haske game da muhimman shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, domin warware manyan batutuwan dake jan hankulan sassan kasa da kasa, da shiyyoyi daban daban.
- Xi Ya Amsa Wasikar Da Tawagar Jami’an ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Suka Aike Masa
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Asusun Merieux Na Kasar Faransa
Ya ce a matsayin ta na babbar kasa mai hangen nesa, har kullum kasar Sin na fara duba kan abun da ya dace da wanda bai dacewa, kan duk wasu batutuwa, tana kuma cimma matsaya ta kashin kan ta. Har ila yau, a matsayin ta na muhimmin karfi na wanzar da zaman lafiya da daidaito, Sin na nacewa samar da mafita a harkokin duniya.
Wang Yi ya kara da cewa, da fari kasar Sin na tunkarar muhimman batutuwa ta hanyar martaba dalilan kafuwa, da ka’idojin MDD. Kana na biyu tana shiga a dama da ita a fannin yayata hawa teburin shawarwari. Sai kuma na uku, wato Sin na tabbatar da an magance damuwar dukkanin sassa dake takaddama da juna. Na hudu kasar Sin na nacewa manufar tasirin sassa daban daban bisa gaskiya, tana kuma adawa da kafa kananan gungu, dake haifar da fito na fito tsakanin bangarori daban daban. (Mai fassara: Saminu Alhassan)