Tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta Tsakiya, Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai danganta matakin da gazawar shugabancin jam’iyyar da manufofin tattalin arziƙin gwamnati da suka jefa ‘yan ƙasa cikin ƙunci.
A wata wasika mai zafi da aka rubuta ranar 28 ga Yuli, 2025, Yar’adua ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin APC saboda rashin gaskiya da cin hanci da ya ce ya mamaye gwamnati, yana mai cewa jam’iyyar ta miƙa wuya ga buƙatun ‘yan tsiraru a maimakon talakawa da suka zabe su.
- Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a
- Gwamnatin Katsina Ta Fara Bayar Da Maganin Zazzabi Kyauta A Asibitoci
Ya bayyana cewa shi da wasu ’yan gwagwarmaya sun sadaukar da kansu wajen gina jam’iyyar CPC da kuma kafa APC, amma yanzu jam’iyyar ta lalace kuma ta juya daga kishin talakawa zuwa jam’iyyar da ke cin zarafin jama’a.
Yar’adua ya bayyana cewa ba zai iya cigaba da zama cikin jam’iyyar da ta kauce daga asalin manufar ta ba, yana mai kiran magoya bayansa su biyo shi zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wacce ya ce na da cikakkiyar tsari don sauya salon siyasar Nijeriya.
Wannan sauya sheƙa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun fushi da rashin jin daɗi a tsakanin manyan ‘yan siyasa kan yadda gwamnati ke tafiyar da harkokin tsaro da tattalin arziƙi a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp