Wani Matashi mai suna Dauda Sa’idu mazaunin unguwar Yelwa, dan shekara 21 a duniya, ya fada tarkon ‘yansanda a jihar Bauchi bisa zarginsa da bin dare ya na farfasa Kaburburan da aka bisne matattu domin samun karfen rodi.
Daga cikin dalilin wanda ake zargin na yin hakan shi ne domin samun damar sayar da rodunan domin samun kudaden sayen abinci da tabar wiwi.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Manoma 6 Da Aka Sace A Katsina
- Dalilin Da Ya Sa Na Dakatar Da Sanusi A Matsayin Gwamnan CBN – Jonathan
‘Yansanda dai su na zargi matashin da kutse cikin makabarta, barnata kabura da kuma laifin sata.
‘Yansanda sun ce, wanda aka tsaren ya kasance na bin tsakiyar dare wajen shiga cikin makabartar Kiristoci da ke Yelwan Kagadama a cikin garin Bauchi ta barauniyar hanya, inda ya janyo lalata kabura da daman gaske da kuma cire rodunan da aka yi amfani da su wajen biso.
A wata sanarwar manema labarai da Sufuritandan dansanda, Ahmed Muhammed Wakil, jami’in watsa labarai na rundunar a jihar Bauchi ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, bayan tuhumar da suka yi da tambayoyi ga Sa’idu, ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Shi dai Sa’idu ya ce, ya cire rodunan da dama inda yake sayar da su kama daga N9,500, N12,000, har 5,500, bi-da-bi.
Saidu ya kuma fada cewa yana amfani da kudaden wajen sayen tabar wiwi da kayan abinci domin amfanuwarsa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya umarci a gurfanar da Sa’idu a gaban kuliya mance sabo da zarar aka kammala gudanar da bincike.
Kwamishinan ya bayyana muhimmancin da ake akwai na iyaye suke sanya lura kan motsin ‘ya’yansu a kowani lokaci.