An samu wani tsohon akanta a ofishin shugaban ma’aikata na Nijeriya, Garba Abdullahi Tahir da laifin wawushe kudin fansho da ya kai Naira miliyan 26 inda kuma aka yanke masa hukuncin shekara 21 a gidan yari.
EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa, ce ta gurfanar da Garba Abdullahi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu laifuka bakwai da ke da alaka da almundahana.
- Sin Ta Nuna Adawa Da Matakin Amurka Na Neman Cin Zalin Kamfanonin Sin
- Me Ya Sa “Fitilar hakkin bil’adam” Ba Ta Haskaka Yara Ma’aikata Masu gwagwarmaya A Kasa Ba?
Da yake yanke hukunci, alkali Inyang Ekwo, ya ce EFCC ta tabbatar da tuhumar da ta ke yi wa tsohon akantan, inda kuma aka same shi da laifin aikata duka laifukan.
Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin daurin shekara uku-uku a kan dukkanin laifukan bakwai, jumulla ke nan zai shafe shekara bakwai a gidan maza.
Wata sanarwa da kakakin EFCC, Wilson Uwajaren ya fitar ta ce tun farko wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifukan da aka tuhume shi da su.