A ranar Alhamis ne wata kungiyar dalibai ta Arewacin Nijeriya ta nada dan wasan kulob din Leicester City, Ahmed Musa, sarautar Jagaban matasan Arewa a Kano.
Abokan arziki na ci gaba da taya dan kwallon Nijeriya Ahmed Musa, murna bayan da aka nada shi sarautar Jagaban Matasan Arewa a birnin Kano da ke Areacin kasar.
A ranar Alhamis ne wata kungiyar dalibai ta Arewacin Nijeriya ta bai wa dan wasan, wanda ke taka leda a kulob din Leicester City, wannan sarauta.
Matasa da dama ne da abokan arzikin Ahmed suka halarci bikin.
Har ila yau, dan wasan, wanda a baya ya murza-leda a kulob din Kano Pillars, ya bude wani wurin wasanni ciki har da wasan kwallon kafar ‘yar tile.