Connect with us

ADABI

Wasu Fuskokin Makwabtaka A Kasar Hausa (II)

Published

on

Ci gaba daga makon jiya

Wannan ya sanya yaranta duka ba wanda ya yi karatun boko bare ma na Muhammadiyya. Ba su da tarbiyya, ga shaye-shaye sun a yi, ga yawan jan fada, ga rashin kunya ga magabaa. Kai, abin ya yi yawa, wai shege da hauka. Sai akan Umme direba shi da iyalansa na gane Malam Bahaushe ba shi da tsarin rayuwa, bas hi da tunanin makomarsa, ba shi tunanin haduwarsa da Allah, bai kuma san darajar kyautar ‘ya’ya da Allah Ya ba shi ba. Haka Umme ya mirgina ya yi ta rayuwa cikin kazanta da jagwalgwalo da alhaki wanda ba ya misaltuwa. Ranar da ya gama dandinsa ya komo Kacina, ya sauka can Tudun Malamai ya na dauke da ‘yan kunshin kayansa kamar almajiri ya tarar sun tashi, sai da aka yi masa jagora aka kaishi inda su ka koma, nan Tudun Galadima. Ya dawo gida ba komi, bai tara komi ba, bai kuma zo da komi ba, bai kuma baro ma kowa ajiya ba, sai suturar da aka ma bashi kwance. Ka ga dandi ba ta yi kyau ba, abin ya zama ranin cilkowa.

Mi aza ya faru, a gida ‘ya’yansa ba su gaishe shi, ba ya da ikon ya sanya su aiki ko ya aike su, su na ma iya zaginsa. Dama na san za a rina, wai an saci zanen mahaukaciya. Kullum sai fada shi da su, har ma Indodo na ce masa ya koma inda ya fito ai ba su ce ya dawo ba. Matata tasha shiga ta raba su fada ma. Sai ta iske suna zagin juna, ya na cewa ‘ubanki na ce’, ita kuma Indodo ta na cewa ‘ubanka na ce’. Ga kuma gandama-gandaman ‘ya’ya a gabansu.  Ka ga girma ya yi gardama. Ga shi a shekaru ya kai 60, amma na banza, na asara.

To a kan haka na zo unguwar na same su. Can da zama ya fara yin tsami ko yami, yaran mu su ka fara yin fada a tsakanin su, maimakon Indodo ta raga mana saboda zaman arziki da mu ka yi sai ta biye ma ‘ya’yanta. Su ka yi ma juna kaca-kaca ita da matata. Shi kuma, da yak e yawon Duniyar tasa yawon banza ne, yawon jahilci sai ya rika biye ma matar. Nan ma mu ka bata. Da, da farko na yi ta yi masa kashedi da cewa kada ya biye ma matarsa, amma inaaaa, ya yi nisa bay a jin kira. Sabili da ma matar na iya korar sa daga gidan matukar bai goyi bayanta ba, saboda ko guntun bulo ba ya da shi a cikin gidan. Da mu ka yi zuwa kimanin 5 caji ofis an ki sasantawa da iyalina da nasa sai ‘yan sanda su ka ba ni shawara tunda shi matsiyaci ne ba ya da arzikin da za ya iya tashi ya gusa y aba ni wuri, ni in tashi in bas hi wuri. Dole na nemi gidan haya na tashi na bar unguwar ina ji ina gani na bar gidan, nawu a kaina na koma can. Wannan shi ne halin Malam Bahaushe mutumin arewa wanda ya tashi cikin tsiya da talauci, na rashin sanin darajar makwabci. Ko uwarka za ka yank aka bashi randa ya tashi yi maka wulakanci sai ka gwammace kida da karatu, don shi abin da za ya duba ‘don mi ya sa za ka fi shi arziki?’Kiri-kiri Bahaushe ya ki Allah wai ya rasa wanda za ya ci ma fuska sai makwabcinsa mai taimakonsa da abin da ma za ya ci ko suturar da za ya daura a gindinsa. Ga mata da rashin tunani, rashin hankali. Don abu kadan sai ya sa ta tada tada hankali, duk a bata da makwabta, su kuma maza ga saurin biye ma mata. Wanda duk ya biye ma mace da karamin yaro, to ba za ya taba zama lafiya ba, kamar dai yanda Umme yabiye ma matarsa Indodo su ke ta fada da mutanen unguwa kullum. Idan an gama da mutanen unguwa sannan su dawo a cikin gida su kuma su yi a tsakanin su, saboda masu iya Magana sun ce duk dan da ya hana uwarshi barci, to tabbace hakika shim aba za ya yi ba.

Ga shi (Umme) nan dan iska tanbadadde, watsatstse, wahalalle, asararre, algungumi, munafiki, malalaci, tsinanne, maras Imani, maras hankali, kullum shi ne sai dai ya tafi kasuwa wajen abokansa ya zauna, a wuni ana zagin mutane. In kuma ya dawo, ya hawo kabu-kabuKo taguwar kirki ba ya da ita, kullum cikin dauda, ciki cike da bakin ciki da nukura. Allah sa mu gane gaskiya. Allah Ka raba mu da rayuwa irin ta Umme direba.

 

Mu kwana nan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: