Wasu Magungunan Kwari Na Manoma Na Da Illa Ga Jama’a – Bincike

Wani masani kuma mai bincike a fannin magungunan kwari da ke sashin nazarin tsirrai a jami’ar Bayero da ke a jihar Kano ya bayyana magungunan kwari da manoma ke amfani da su da cewa na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da illa ga lafiyar jikin yan dam.

Alhaji Murtala Ya’u ne ya bayyana hakan a wani taron bita da ka shiywa manoma a jihar Kano.

A cewar sa, daga cikin illolin da magungunan ke haifarwa akwai cutar ciwon koda ciwon Hanta, wanda suna daya daga cikin cutukan da mutane ke fama da su a yanzu.

Shima a nasa jawabin a gurin taron, Sarkin Noma na jihar Kano Alhaji Yusuf Na-Dabo yace rashin kula da yadda za’ayi amfani da magugunan na daya daga abinda yake kawo gurbacewar kayayyakin noma.

Sarkin Noman ya kuma bukaci manoma da su rinka baiwa gona hutu na dan lokacin, inda ya ce, hakan yana taimakawa wajen samun kyakyawan amfani gona.

Exit mobile version