A yayin da wani sashi na kwayoyin halittar kwakwalwa (Brain cells), suka mutu, wani sashin na iya karbar aikinsu. Wannan shi ne abin da ke faruwa a kwakwalwar mai shanyewar barin jiki, ta yadda motsin hannu ko kafa kan dawo bayan ya shanye.
Kwakwalwa ba ta dauke da maganadisin jin ciwo (Pain receptors), shi yasa kwakwalwa ba za ta iya jin ciwo kamar yadda sauran sassan jiki ke jin ciwo ba. Don haka, ciwon kai na zuwa ne daga sauran sassan da ke kewaye da kwakwalwa, amma ba kwakwalwar kanta ce ke ciwo ba.
- Mata A Dage Da Karatu Yin Haka Taimakon Kanku Ne Da ‘Ya’yanku – Zainab Ahmad
- CMG Ta Zanta Da Shugaban Kasar Brazil
Kwakwalwa ta fi kowane sashin jiki son kanta. Dalili kuwa, duk da cewa nauyinta ba ya wuce kashi uku cikin dari (3%) na nauyin jikin mutum, amma dole sai an ba ta kashi talatin cikin dari (30%) na yawan jinin da zuciya ke turawa a kowane bugu.
A mafi yawan lokaci, Dan’adam na amfani da dukkanin sassan kwakwalwarsa, sabanin tatsuniyar da ke cewa; wai Dan’adam na iya amafani da dan wani sashi na kwakwalwarsa ne kawai a tsawon rayuwarsa.
Kusan rabin sinadarin abincin da yara ke ci, na tafiya ne wajen gina kwakwalwarsu; domin koyon abubuwa daban-daban.
Kamar yadda motsa jiki ko atisaye ke kara lafiyar jiki, haka nan ma yake kara lafiyar kwakwalwa.
Kamar yadda tambarin babban yatsan hannunka (thumbprint) yake daban da na kowa, haka ma yadda kwakwalwarka ke aiki daban da ta kowa.
Har ila yau, kwakwalwa na aiki ne da tsarin lantarki a yayin da mutum yake a farke, kazalika kwakwalwa na iya samar da karfin lantarkin da zai iya kunna farin kwai na lantarki.
Kimanin kashi sittin cikin dari (60%) na kwakwalwa kitse ce.
Har wa yau, rashin isassshen barci na rage kaifin kwakwalwa. Domin kuwa, Dan’adam na bukatar barci na kimanin awa bakwai zuwa tara a kullum.
Kwayoyin halittar kwakwalwa, ba sa iya jure rashin iskar oksijin da sinadarin gulukos na fiye da minti biyar, face sai sun mutu.