Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Watakila Barcelona Ta Sayar Da Messi A Watan Janairu

by Muhammad
December 26, 2020
in WASANNI
4 min read
Barcelona
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ana ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta da juna a tsakanin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona akan ci gaba da rike dan wasa Messi ko kuma sayar dashi a watan Janairu mai zuwa.

Tuni dai wasu daga cikin masu neman shugabancin kungiyara suka fara nuna ra’ayoyinsu akan dan wasa Messi ya yinda wasu suke ganin lokaci yayi da zasu sayar da dan wasan a watan janairu wasu kuma daga cikin ‘yan takarar suke ganin zasu shawo kan dan wasan ya ci gaba da zaman kungiyar.

samndaads

Duk da cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta nisanta kanta da zawarcin dan wasan Barcelona, Leonel Messi, wanda ake ta rade radin cewa zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana ko kuma cikin watan Janairu mai zuwa har yanzu ana ci gaba da alakanta dan wasan da zakarun na kasar faransa tare da Manchester City.

Tun farko dai burin dan wasa Messi shi ne barin Barcelona a farkon wannan kaka sai dai burin nasa bai cika ba sai dai  ana ganin lokaci yayi da dan wasan zai fara tattaunawa da wasu daga cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa.

A cikin watan Agustan daya gabata kungiyar kwallon kafa ta  Manchester City ta so daukar dan wasa Lionel Messi daga kungiyar kwallon kafa ta  Barcelona, bayan da dan kwallon ya bukaci barin kungiyar sakamakon rashin jituwa da tsohon shugaban gudanarwar ta Barcelona.

Barcelona ta ci karo da cikas a kakar bara, bayan da ta kasa lashe kofi ko guda daya, da kuma  dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League daci 8-2.

Kyaftin din tawagar na Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu – wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoban daya gabata wanda hakan yasa dan wasan ya bukaci raba gari da kungiyar wadda ya fara bugawa wasa tun yana matashi.

Kwantiragin Messi zai kare a kungiyar Barcelona a karshen watan Yunin shekarar 2021, wanda hakan na nufi wata kungiyar za ta iya tattaunawa da shi da nufin daukar shi ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

Wannan dama ce idan Manchester City za ta yi amfani da ita wajen sake zawarcin kyaftin din Argentina sai dai wasu bayanai na cewa Manchester City  ba za ta iya biyan Barcelona Yuro miliyan 50 ba, kudin da kungiyar za ta amince saboda halin matsi da cutar korona ta haddasa.

Ana ganin  Manchester City za ta iya jira zuwa karshen kakar bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Camp Nou kuma zai tafi ba tare da kungiyar ta Barcelona ta samu ko sisin kwabo ba sai dai kuma yawan albashin da yake dauka zai hana wannan ciniki.

Tuni dai Manchester City ta haura da zawarcin dan wasan saboda yana daukar yuro miliyan 100 wanda ba karamin kudi bane a halin yanzu da kungiyoyi suka talauce sakamakon annobar cutar Korona hakan yasa dole zasu hakura da daukar dan wasan.

Bugu da kari shugabannin kungiyar kwallon kafa ta PSG suna ganin idan suka dauki Messi ya koma kungiyar zasu samu damar ci gaba da rike Neymar sannan shima matashin dan wasa Mbappe zai iya zama idan har yaga Messi ya koma kungiyar.

A kwanakin baya ne Mbappe ya sanar da shugabannin kungiyar cewa zai iya barin kungiyar a karshen kakar wasa inda tuni kungiyoyin Jubentus da Real Madrid da Liberpool suka fara nuna sha’awarsu ta ganin sun dauki Mbappe, dan Faransa.

Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi a cikin watan Janairu domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.

Sai dai banda Manchester City, kungiyoyin Chelsea da Inter Milan da kungiyar Bayern Munchen duka sun nemi Messi sai dai a halin yanzu ana ganin PSG ce akan gaba wajen neman kaftin din na Barcelona da Argentina.

Shin Messi Zaiyi Abin Kirki A Faransa Ko Ingila?

Sai dai an fara nuna shakku akan ko tauraruwar dan wasa Messi zata ci gaba da haskawa a daya daga cikin kasashen  Ingila ko Faransa inda ake tunanin zai koma daya daga cikinsu amma kuma wasu suna ganin Messi gwarzon duniya ne saboda haka duk inda yaje zai nuna kansa.

A kowanne wasa a fadin duniya akwai matakin da ake zuwa dan wasa yayi ritaya daga buga wannan wasan ko kuma wasan yayi ritaya daga jikin dan wasan idan ya kasa ganewa cewa lokaci yayi da zai koma gefe ya huta domin ya bawa wasu dama.

Hakane ne yasa ‘yan wasa da dama suke ajiye takalmansu da zarar sunga kwallon ta fara tafiya daga kafarsu ko kuma da zarar sunga shekaru sun fara yi musu yawa kuma an fara samun matasa masu tasowa.

A kwanakin baya Messi ya bukaci barin Barcelona sakamakon rashin jituwar daya samu tsakaninsa da shugaban gudanarwar kungiyar Josep maria Bartemeu wanda a karshe ya ajiye mukamin nasa a farkon  watan daya gabata.

Sai dai shugaban kula da gasar La Liga ta kasar Sipaniya, Javier Tebas ya bayyana cewa a shirye yake idan har  Messi ya bar kasar Spaniya da buga wasanninsa saboda manyan ‘yan wasa a baya sun buga gasar kuma sun tafi ba tare da sun samu nakasu ba

Messi ya bukaci izinin barin Barcelona a cikin watan Agustan daya gabata  kungiyar da ya je tun  yana da shekara 13 daga baya batun ya lafa, bayan da aka tsawaita yarjejeniyar zamansa a Barcelona na tsawon shekara daya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Na Gama Shirin Fafatawa Da Tyson Fury -Anthony Joshua

Next Post

Matasa Ne Tubalin Gina Ci Gaban Kasa

RelatedPosts

Lukaku

Za Mu Iya Lashe Gasar Siriya A – Lukaku

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan,...

Pogba

Mun Shirya Doke Liverpool, Cewar Pogba

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul...

Mourinho

Mourinho Ya Caccaki ‘Yan Wasansa

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Kociyan kungiyar Tottenham, Jose Mourinho ya koka da rashin kokarin...

Next Post
Matasa

Matasa Ne Tubalin Gina Ci Gaban Kasa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version