Abba Ibrahim Wada" />

Watakila Rashin Zuwa Gasar Zakarun Turai Yazama Alheri Ga Chelsea –Hazard

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, ya bayyana cewa rashin zuwan Chelsea gasar zakarun turai watakila ya sake zamarwa kungiyar alheri a kakar wasa ta gaba saboda za su samu karancin wasanni.

Hazard ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labara inda yace tabbas kakar wannan shekarar batazo musu da sauki ba saboda suda suka zama zakara a shekarar data gabata amma kuma yanzu sune suke zaune a matsayi na biyar.

Ya kara da cewa amma a kakar data gabata basu buga gasar ba ta zakarun turai amma kuma sun lashe kofin firimiya saboda haka watakila ma wanann kakar hakan ta kasance.

Ya kara da cewa kungiyar Chelsea kungiya ce wadda koda yaushe kokarinta shine lashe kowacce irin gasa saboda haka duk da haka akwai gasar cin kofin kalubale a gabansu kuma za suyi iya yinsu domin ganin sun lashe gasar.

A karshe yace har yanzu akwai dama domin saura wasanni shida a gasar kuma wadda take mataki na hudu tabasu maki 10 saboda haka za su ci gaba da lashe wasanninsu har sai sunga abin da ya turewa buzu nadi.

A wasan da Chelsea dai ta buga da kungiyar Westham Chelsea ta buga 1-1 har gida wanda wannan sakamakon wasanne ya sake tabbatarwa da kungiyar cewa abune mai wahala kungiyar ta iya zuwa gasar zakarun turai.

 

Exit mobile version