Nijeriya a hukumance ta shigar da allurar rigakafin cutar HPV a cikin tsarin rigakafinta na yau da kullum, da nufin kai wa yara mata miliyan 7.7 agaji cikin zagaye guda na allurar rigakafin cutar, wanda ya kasance mafi girman irinsa a yankin Afirka.
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Ali Pate, ya bayyana matukar damuwarsa kan cutar ta kansar mahaifa, yana mai cewa, “Asarar mata kusan 8,000 a duk shekara daga cutar da ake iya rigakafinta ba abu ne da za a amince da shi ba.“.
- CMG Da WIPO Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa
- Ganduje Ya Yaba Da Hukuncin Kotun Koli Akan Nasarar Zaben Tinubu
Pate ya jaddada cewa ceton rayuka da tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya su ne jigon kudirin inganta lafiyar al’umma na shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa, “A matsayina na uba, ni kaina, ina da ‘ya’ya mata hudu, dukkansu sun yi allurar rigakafin cutar HPV guda daya don kare su daga cutar kansar mahaifa.
“Ina so in yi kira ga ‘yan uwanmu iyaye da su tabbatar da cewa ‘yan matanmu sun amshi allurar rigakafin kamuwa da cutar kansar mahaifa”.
‘Yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 za su sami kashi ɗaya na maganin rigakafin na HPV, wanda yake da tasiri wajen hana kamuwa da cutar.
Daga nau’ukan maganin rigakafin akwai HPV 16 da 18.
Cutar kansar mahaifa ita ce ta biyu da take sanadin mutuwar mata masu shekaru 15 zuwa 44.
Wakilin WHO a Nijeriya, Dokta Walter Kazadi Mulombo, ya ce, “Wannan wani muhimmin lokaci ne a kokarin da Nijeriya ke yi na rage yawaitar kansar mahaifa – daya daga cikin cutar kansar da za a iya kawar da su ta hanyar alluran rigakafi.”
“Mun himmatu wajen tallafa wa gwamnati ta kara samun damar yin amfani da allurar rigakafin cutar ta HPV don kare lafiya da jin dadin rayuwar mata a nan da wasu shekaru masu zuwa.“.
UNICEF ta taka muhimmiyar rawa a wannan shiri, inda ta siyo rigakafin cutar ta HPV kusan miliyan 15 a madadin Gwamnatin Nijeriya. Bugu da kari, UNICEF ta samar da kayan fadakarwa da suka hada da radiyo da tallace-tallace na Talabijin a cikin harsunan gida da yawa don kawar da jita-jita game da rigakafin.
Taron kaddamar da shirin rigakafin na tsawon kwanaki biyar, ya kunshi makarantu da al’umma a fadin jihohi 16 da kuma Abuja.
A haka kuma, maganin zai zama wani ɓangare na tsarin rigakafi na yau da kullum a cibiyoyin kiwon lafiya.
Ana sa rai Kashi na biyu zai fara aiki a watan Mayun 2024, wanda zai ƙunshi jihohi 21.
Ana yin allurar rigakafin cutar HPV kyauta, wanda Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya, tare da tallafin Gidauniyar Gavi, the Vaccine Alliance, UNICEF, WHO, da sauran abokan haɗin gwiwa suka haɗa hannu suka samar.