Yau Litinin 13 ga wata ne, aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojan kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cikin jawabinsa yayin bikin rufe taron cewa, amincewar da jama’ar suka nuna masa, ta karfafa masa gwiwar neman samun ci gaba, wadda kuma shi ne nauyin da ke wuyansa. Xi ya kara da cewa, zai yi iyakacin kokarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora masa. Zai kuma yi aiki tukutu bisa bukatun kasa, da muradun jama’a. Bugu da kari, zai sadaukar da kansa. Ba zai kuma ci amanar wakilan jama’a masu halartar taron da kuma daukacin al’ummomin kabilun kasa ba.
Xi Jinping ya jaddada cewa, za mu ci gaba da raya kasar Sin mai karfi gami da farfado da al’ummar Sinawa, kamar yadda kaka da kakaninmu suka yi a baya. Xi ya bayyana cewa, al’ummar Sinawa sun cimma gagaruman nasarori a tarihi, tare da jure wahalhalu masu yawa. Bayan kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta hanyar hada kan al’ummomim kabilu daban daban na kasar da kuma ba da jagora wajen yin gwagwarmaya har tsawon shekaru fiye da 100, don sake dawo mutuncinmu. Al’ummar Sinawa sun dawo da makomarsu a hannunsu. Al’ummomin Sinawa sun sake tsayawa da kafaffunsu, sun samu wadata. Yanzu suna kokarin raya kasarsu mai karfi. Ba wanda zai iya hana babban sha’anin farfado da al’ummar Sinawa. Kar a ci amanar jama’a. Wajibi ne a shugabanni su sauke nauyin da zamani da kuma tarihi ya dora musu, su ba da tasu gudummowa wajen kara azama kan raya kasar Sin mai karfi da farfado da al’ummar Sinawa, kamar yadda kaka da kakaninsu suka yi a baya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, yayin da ake raya kasar Sin mai karfi, tilas ne a karfafa raya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ko da yaushe a tafiyar da harkokin jam’iyyar a tsanake ba tare da kasala ba, kuma a kara yin yaki da cin hanci da karbar rashawa ba kakkautawa.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, za a yi kokarin zamanintar da harkokin tsaron kasa da ma rundunar sojan kasar, ta yadda rundunar sojan kasar za ta taka rawar da ta kamata wajen kare ikon mulkin kai da tsaro da moriyar ci gaban kasar.
Xi Jinping ya ce, ci gaban kasar Sin na haifar da alfanu ga duniya, kuma kasar Sin ba za ta iya ware kanta da sauran kasashen duniya wajen tabbatar da ci gabanta ba. Kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga duniya, da yin amfani da kasuwanni da ma albarkatu na duniya don raya kanta, tare kuma da sa kaimin ci gaban duniya baki daya.
Xi Jinping ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ci gaba mai inganci da kuma mai da jama’a a gaban kome, a kokarinta na raya kanta da ma farfado da al’ummar kasar, za kuma ta yi kokarin tabbatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki iri biyu” da dinkuwar kasar baki daya, tare da kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. (Tasallah Yuan & Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp