Da safiyar yau Talata ne aka bude zaman farko na taron kolin G20, a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, ya kuma gabatar da jawabi.
A jawabin nasa Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar babban kalubalen raya kasashen duniya. Don haka ya kamata mambobin G20 su sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na manyan kasashen duniya, domin neman bunkasuwar kasa da kasa, da tallafawa alummun duniya, yayin da ake tabbatar da ci gaban duniya baki daya.
Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa suna fuskantar kalubalen raguwar tattalin arziki. Don haka ya ba da shawarar kafa dangantakar abokantaka ta neman farfado da tattalin arzikin duniya, da mai da aikin neman ci gaba, da raya alumma a matsayin babban aikin da aka sanya gaba, tare da mai da hankali kan bukatun kasashe maso tasowa.
Kaza lika ya ce kasar Sin tana goyon bayan shigar da kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU kungiyar G20.
Haka kuma, cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata a nemi ci gaban da kowace kasa za ta iya cin gajiya. Ci gaban da kowace kasa za ta ci gajiya tare, hakikanin ci gaba ne da ake bukata. Ya kamata kasashen dake kan gaba wajen samun ci gaba, su ba da taimako yadda ya kamata ga sauran kasashe, da kuma samar musu karin damammakin da suke bukata.
Ya ce, Kalubaloli masu tsanani da ake fuskanta wajen neman bunkasuwar kasashen duniya, su ne babu isashen hatsi da makamashi.
Kuma, muhimmiyar hanyar da za mu yi amfani da ita wajen shawo kan wadannan kalubaloli ita ce, yin hadin gwiwa kan aikin sa ido a kasuwanni, da kuma kafa manyan kasuwannin bude kofa ga waje, domin karfafa tsarin samar da kayayyaki cikin hadin gwiwa, da kuma daidaita farashin kayayyaki yadda ya kamata.
Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, a yayin babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 20 da aka yi watan jiya, an tabbatar da burin ci gaban kasar Sin da na JKS cikin shekaru 5 masu zuwa.
Kuma kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman bunkasuwa cikin lumana, da zurfafa aikin kwaskwarima, da kuma kara bude kofa ga waje, domin neman farfadowar kasar Sin baki daya ta hanyar zamanintar da kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)