A safiyar yau Alhamis 4 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.
A yayin ganawar, Xi Jinping ya nuna cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Faransa su sauke nauyin dake bisa wuyansu, da bin ra’ayin kasancewar bangarori da dama, kana da tsayawa kan matsayin daidai. A cewarsa, kasar Sin na son yin aiki tare da bangaren Faransa, don tsayawa kan tattaunawa bisa tushen zaman daidai-wa-daida, da bude kofa, da ma gudanar da hadin gwiwa, ta yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta samu ci gaba yadda ya kamata, bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a cikin shekaru 60 na sabon zagaye.
Baya ga haka kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata ko da yaushe kasashen biyu su yi hangen nesa, da kare ’yancin kai bisa matsayinsu na manyan kasashe, da nuna fahimta, da goyon bayan juna kan muhimman batutuwan dake jawo hankulansu duka. Xi ya kara da cewa, kasashen Sin da Faransa, duka su kasance mambobi yayin kafuwar MDD, kana zaunannun kasashe membobin kwamitin sulhu na MDD, don haka ya kamata su kiyaye tsarin kasa da kasa dake mayar da MDD ginshiki, kuma bisa tushen dokokin kasa da kasa, da karfafa yin cudanya, da hadin kai a fannin warware rikici ta hanyar siyasa, da inganta zaman lafiya da zaman karko na duniya, kana da sa kaimi ga ayyukan kwaskwarima da nufin kyautata harkokin duniya baki daya.
A nasa bangaren, shugaba Macron ya bayyana cewa, har kullum Faransa da Sin suna yin mu’amala sosai tsakanin shugabanninsu, kuma suna nuna amincewa da girmama juna. Kazalika kasarsa na dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar ta Sin, tana kuma tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, tana mai fatan zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkannin fannoni tsakanin kasashen biyu.
Bayan shawarwarin, sun halarci bikin sanya hannu kan wasu takardun hadin kai da dama, da suka shafi makamashin nukiliya, da hatsi, da ilmi, da ma muhallin halittu da dai sauransu a tsakanin kasashensu biyu.
Baya ga haka, shugabannin kasashen biyu sun gana da manema labaru na Sin da kasashen waje tare, inda baki daya suka amince da karfafa amincewa juna, da habaka hakikanin hadin kai, da kara yin cudanyar al’adu, da kuma inganta yin kwaskwarima don kyautata ayyukan gudanar da harkokin duniya.
Kafin shawarwarin, shugaba Xi Jinping da uwar gidansa madam Peng Liyuan, sun shiryawa Macron da uwar gidansa Brigitte Macron bikin maraba da zuwansu. Har ila yau, da tsakar ranar yau Alhamis shugaba Xi Jinping da Peng Liyuan sun shiryawa Macron da Brigitte liyafar maraba.
Hakazalika, shugabannin biyu sun halarci bikin rufe taro na bakwai na kwamitin mamallaka masana’antu na kasashen Sin da Faransa, tare kuma da gabatar da jawabai. (Bilkisu Xin)














