A ziyarar da ya kai jihar Mongoliya ta gida a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya zama wajibi a mai da hankali kan aikin farko na sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci, da kiyaye tsarin fifikon muhalli, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, a kokarin rubuta wani sabon babi na zamanintar da jihar.
Xi Jinping ya ce, jihar Mongoliya ta gida wani muhimmin tushe ne na makamashi da albarkatu da kayayyakin gona da dabobbi na kasar, don haka ya kamata a yi wa sana’o’i garambawul bisa matsayinsu, da kara karfin bunkasa wasu muhimman sana’o’i, da kuma kokarin fito da wata sabuwar hanyar canja salon bunkasuwar tattalin arziki a yankin dake da rinjaye a fannin albarkatu da makamashi, har ma da gaggauta kafa tsarin zamanintar da al’ummar jihar bisa la’akari da halin da jihar ke ciki.
Xi Jinping ya kara da cewa, tabbatar da tsarin kiyaye muhalli a arewacin kasar, shi ne aikin dake gaban jihar wadda ke da babbar ma’ana ga kasar.
Dole ne a kara karfin yaki da kwararruwar hamada da kiyaye fadamu, da ingiza karfin hana gurbatar iska da ruwa da kasa, ta yadda za a kafa tsarin kiyaye muhalli a wurin dake amfanawa fadin kasar.
Ban da wannan kuma, Xi ya ce, ana fuskantar kalubaloli da dama lokacin da ake ingiza aikin samun wadatar al’umma tare a wurare dake dab da iyakokin kasar.
Don haka, ba za a bar kowa a wadannan al’ummomi a baya ba yayin da ake kokarin samun wadatar al’umma baki daya. (Amina Xu)