A gabannin babban taron gamayyar kungiyoyin masu aikin sa kai ta kasar Sin karo na uku, babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping ya aika da wasika don taya murnar kiran taron, inda ya mika gaisuwa ga masu aikin sa kai da kungiyoyin aikin sa kai da ma ma’aikatan kula da ayyukan sa kai.
A cikin wasikar, shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, aikin sa kai muhimmiyar alama ce ta ci gaban wayewar kan al’umma, kana muhimmiyar hanya ce ga masu aikin sa kai su hidimtawa sauran mutane, da ma bautawa zaman al’umma. Yana mai fatan ganin masu aikin sa kai da kungiyoyin aikin sa kai da ma’aikatan kula da ayyukan sa kai za su karfafa ruhin aikin sa kai, da himmantuwa wajen shiga ayyukan zamanantar da kasar Sin, da kuma yayata halaye masu kyau irin na gaskiya da kirki, kana da ba da gudunmowarsu ga gina kasa mai karfi da farfado da al’umma. (Mai fassara Bilkisu Xin)














