Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin da ake yi na gina ingantattun yankunan cinikayya maras shinge na gwaji (FTZs), inda ya bukaci wadannan yankunan da su zama sahun gaba wajen samar da sabbin damammaki, da tunkarar kalubale masu tsauri.
Xi, ya bayyana hakan ne a cikin wani umarni na baya-bayan nan game da inganta aikin gina yankunan cinikayya maras shinge na gwaji.