Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, a yammacin ranar Juma’a ya jagoranci zama na 40 na taron tattaunawar hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar.
Zaman mai muhimmanci da Shugaba Xi ya shugabanta dai an yi shi ne domin tattauna batutuwa dake shafar yadda za a tabbatar jami’an gwamnati ba su samu wata damar ta’ammali ko nuna sha’awar aikata rashawa ba.(Mai fassarawa: Ahmad daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp