Babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping ya ziyarci jami’ar Xinjiang, da yankin tashar ruwa ta kasa da kasa ta Urumqi, da al’ummar Guyuanxiang dake gundumar Tianshan, da gidan adana kayan tarihi na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta dake birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, daga yammacin ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba.
Xi ya fahimci yadda ake aikin zakulo masu hazaka, da yadda ake daidaita matakan yaki da annobar COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa tare, da inganta hadin kan kabilu da bunkasuwa, da karfafa fahimtar al’ummar kasar Sin, da dai sauransu.
A safiyar ranar Laraba, shugaba Xi ya kuma kalli wani wasan gargajiya na kabilar Kirgiz mai suna Manas, da aka shirya a gidan adana kayan tarihi na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. Inda ya bayyana cewa, kiyaye al’adu irin na Manas, wata al’ada ce ta ‘yan tsirarun kabilu da kuma al’ummar kasar Sin. Yana mai jaddada kara kokarin kiyayewa da yayata al’adu.
Haka kuma shugaba Xi ya ziyarci mazauna garin Guyuanxiang, inda ya ce, dole ne a kara kaimi, ta hanyar dogaro da al’umma. Don haka, ya bukaci hukumomi su kara himma, wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma, don kara koyo da biyan bukatun jama’a da amfanar da mazaunan dukkan kabilu.
Sannan Xi ya ziyarci yankin tashar kan tudu ta kasa da kasa ta Urumqi a yammacin ranar Talata, yana mai cewa, yayin da ake samun ci gaba a hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, a hannu guda kuma, ba za a bar jihar Xinjiang a baya ba, sai ma ya zama yanki mai muhimmanci, kuma wata cibiya. Ya kuma yi na’am da ci gaban da ma’aikatan suka samu, inda ya karfafa musu gwiwar kara kokarin yin aiki don samun gagarumar nasara. (Ibrahim Yaya)