Ana zargin wani mai suna Kadir da tsirewa bayan daba wa kanensa, Suleiman, wuka har lahira a Auchi da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma ta Jihar Edo.
A cewar rahotanni, Suleiman ya tsawata wa matar Kadir ne a ranar Juma’a saboda irin rashin mutuncin da take yi ga mahaifiyarsu, kuma Kadir, wanda ba ya gida a lokacin da rikicin ya faru, ya tunkari kanin nasa ne saboda tsawatarwar da yayi wa matar tasa lokacin da bana nan.
An ce mahaifiyarsu ta shiga tsakani kuma ta sasanta rikicin tsakanin ’ya’yan nata biyu. Amma kuma an ce Kadir ya sake tado da batun a yammacin ranar, inda mahaifiyarsu ta sake shiga tsakani ta kwantar lamarin.
A nasa bangaren, an ce Suleiman ya manta da batun, inda ya cigaba da harkokinsa na yau da kullum. Amma Kadir daga baya an ce ya dabawa Suleiman wuka da yamma kuma ya gudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Princewill Osaigbobo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, mamacin ya mutu ne a asibitin St. Jude, inda aka kai shi don kula da lafiyarsa.