Connect with us

WASANNI

Ya Kamata Blind Ya Koma Barcelona, Cewar Ban Gaal

Published

on

Tsohon mai koyar da yan wasan Manchester United, Luis Ban Gaal yace yakamata dan wasan kungiyar, Danley Blind yafara shirin barin kungiyar domin komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

A hirar da yayi da masu saurare, Ban Gaal ya ce, tunda yanzu kungiyar bata amfani dashi gaba daya yakamata yasan abinyi, yakamata yabar kungiyar zuwa Barcelona domin kwallon Barcelona za ta da ce da irin salon wasan sa.

Ban Gaal yaci gaba da cewa dan wasan yanada tunani mai kyau kuma yana iya buga wurare dayawa acikin fili saboda haka ya canja kungiya indai yanason tauraruwarsa taci gaba da haskawa a duniya.

Ya kara da cewa, Blind dan wasa ne wanda zai iya buga wasa a tsakiyar baya da tsakiyar fili da kuma dan wasan baya amma ta gefen hagu saboda haka duk kungiyar data sameshi zaiyi mata amfani yadda yakamata.

Blind mai shekara 27 a duniya dan asalin kasar Holland yakoma Manchester United ne daga kungiyar Ajad Amsterdam a shekara ta 2014 lokacin da Luis Ban Gaal yana aikin koyarda kungiyar ta United kuma ya taimaka kungiyar ta lashe kofin Europa League a shekarar data gabata a lokacin Jose Mourinho.

Kwantaragin dan wasan dai zai kare ne a karshen kakar wannan shekarar kuma tuni kungiyar ta Manchester United tabashi damar tattaunawa da wasu kungiyoyin  wadanda suke son daukarsa.

A kwanakin baya dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta taya dan wasan yayinda tsohuwar kungiyarsa ta Ajad itama tafara zawarcin dan wasan ko zai iya komawa kungiyar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: