Gwamnatin Nijeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen yin kira da a kai zuciya nesa kan barazanar Iran da Isra’ila.
Ta bukaci a ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa yaduwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.
- Yawan Na’urori Masu Samar Da Wutar Lantarki Ta Makamashin Nukiliya Da Ake Harhadawa A Sin Ya Ci Gaba Kan Matsayin Farko A Duniya
- Farashin Kayan Masarufi Ya Sake Tashi Zuwa Kashi 33.2 A Nijeriya – NBS
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje, ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga kasashen da su duba batun warware rikici cikin lumana.
Ta ce akwai bukatar samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-daya.
Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin nata a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojinta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai karamin ofishin jakadancin ƙasar a Siriya, ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.
Sai dai harin ya bar baya da kura, inda manyan kasashen duniya suka nuna rashin jin dadinsu game da matakin na Iran
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp