Shugabar kungiyar kare hakkin Bil’adama ta ‘Ban Gaskiya Human Right Inniatibe’ a Jihar Kaduna, Hajiya Aisha Muhammad ta shawarci majalisar Jihar Kaduna da ta tabbatar da dokar da za a hukumta ‘yan baya ga dangi da suke yi wa yara fyade.
Hajiya Aisha ta bayyana haka ne a lokacin da ta zanta da wakilinmu da ke Zariya.
- Ana Zargin Wani Hadimin ‘Yar Majalisa Da Yi Wa Almajiri Fyade A Kaduna
- Fyade: An Yanke Wa Robinho Zaman Gidan Kaso Na Shekara Tara
Ta ci gaba da cewa idan an dubi yadda matsalar fyade ga kananan yara ya zama ruwan dare, ya dace a sami doka mai tsananin da za a rika yin hukumci ga duk wanda aka samu da yi wa kananan yara fyade a daukacin kananan hukumomin Jihar Kaduna 23.
Hajiya Aisha ta kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani idan majalisar jihar ta samar da dokar ya sa hannu, domin samun dama ga kotuna su fara hukunta wadanda aka samu da laifin yin fyade a fadin Jihar Kaduna.
Haka kuma Hajiya Aisha ta shawarce iyaye su fara yin taka tsan-tsan na yadda suke dora wa kananan yara tallafa, wanda ta ce shi ne matsalar da ke zama silar fyade ga kananan yara a Jihar Kaduna da kuma sassan arewacin Nijeriya baki daya.