A jiya Alhamis, shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, ganawar da ta yi matukar janyo hankalin kasa da kasa, a sabili da kasancewarsu kasashen mafiya karfin tattalin arziki a duniya, ganawar ba kawai ta shafi kasashen biyu ba ce, har ma da duniya baki daya.
Sin da Amurka kawayen juna ne ko abokan gaba? Ita ce tambayar da ya kamata a amsa tun farko wajen daidaita huldar da ke tsakanin kasashen biyu. A yayin ganawar ta kusan tsawon awa biyu da aka yi a jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da amsa, inda ya ce, ya kamata Sin da Amurka su kasance kawayen juna, tarihi ne ya shaida mana haka, kuma hakan abu ne da ake bukata a zahiri.
Ba shakka, sakamakon yadda Sin da Amurka suka sha bamban da juna ta fannoni daban daban, ba za a rasa samun sabani a tsakaninsu ba. Amma ya kamata a lura da cewa, kasashen biyu suna da babbar moriyar bai daya da ta zarce sabani a tsakaninsu, sakamakon yadda suka shafe shekara da shekaru suna kulla alakar kut da kut da juna musamman ta fannin tattalin arziki da cinikayya, kuma yin hadin gwiwa da juna hanya ce madaidaiciya daya tilo gare su, in ba haka ba, kowacensu za ta tafka mummunar hasara in sun yi gaba da juna. Kamar dai yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, babu sabani a tsakanin burin kasar Sin na bunkasa kanta da kuma burin da shugaba Trump ke neman cimmawa na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi” (MAGA), kasashen biyu za su iya cin gajiyar nasarar juna tare da tabbatar da ci gaba mai albarka na bai daya.
Sai dai don neman cimma burinta na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi”, kasar Amurka ta sha daukar matakai na dakile ci gaban kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da ma sanya takunkumai ga kamfanoninta masu ci gaban kimiyya da sauransu, duk da hakan, kasar Sin ta kiyaye bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, har ma karuwar tattalin arzikinta ta kai kaso 5.2% a cikin watanni tara na farkon bana, lamarin da ya shaida inganci da juriya na tattalin arzikin kasar. A kwanan nan, kasar Sin ta zartas da shawarwarin da aka gabatar game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma bisa ga shawarwarin, za a tsara shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15 na kasar. Cikin sama da shekaru 70 da suka wuce, kasar Sin ta yi ta kokarin aiwatar da shirye-shiryen ba tare da kasala ba, ba don neman kalubalantar wata ko maye gurbinta ba, amma don mai da hankali a kan raya kanta da kuma bayar da damammaki na samun ci gaba ga sauran kasashen duniya.
Ganawar da aka yi a wannan karo ta kasance ta farko a tsakanin shugabannin kasashen biyu tun bayan da shugaba Trump ya sake hawa karagar mulkin kasar Amurka. Kafin wannan kuma, shugabannin biyu sun taba tattaunawa da juna ta wayar tarho har sau uku, don nuna alkiblar bunkasar huldar kasashensu. Tun bayan watan Mayun da ya gabata, bisa daidaiton da shugabannin biyu suka cimma, tawagogin kasashen biyu sun gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya har sau biyar. A sabon zagayen shawarwarin da aka gudanar a baya bayan nan a birnin Kuala Lumpur, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan tattalin arziki da ciniki da ke janyo hankulansu duka, tare da cimma matsaya daya a kan matakan da za a dauka. Lallai ta hanyar yin shawarwari da juna cikin daidaito, sassan biyu sun kai ga karfafa fahimtar juna da amincewa da juna, hakan kuma ya shaida cewa, yin shawarwari da juna ya fi yin gaba da juna, kuma Sin da Amurka suna iya raya kansu tare da tabbatar da ci gabansu na bai daya.
Kasancewarsu kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, alhakin da ke rataya a wuyan Sin da Amurka ne su gano hanyar da ta dace ta cudanya da juna. Kasashen biyu za su iya karfafa ginshikin huldarsu da samar da kyakkyawan yanayi na bunkasa kansu, tare da samar da karin tabbas da kwarin gwiwa ga duniya, muddin sun tabbatar da daidaiton da shugabanninsu suka cimma, kuma suka yi hangen nesa tare da nacewa ga yin shawarwari da juna wajen daidaita sabaninsu, da kuma inganta hadin gwiwarsu da mu’amala da juna a kai a kai.
			




							








