Ya Kona Budurwarsa Saboda Ta Yanke Alakarsu

Budurwarsa

Wata yarinya tana cikin halin ha’ula’i na rayuwarta bayan da tsohon saurayinta ya cinna mata wuta saboda ta yanke alakarsu.

Yarinyar ‘yar shekaru 13 ta gamu da kuna har kusan kashi 90 na jikinta bayan tsohon saurayin na ta mai shekaru 19 ya zuba ma ta mai a jikin ta sannan ta cinna ma ta wuta.

Wilson Jabier Meléndez Bonilla, mai shekaru 19, ya shiga gidan yarinyar ne da ke kudu maso yammacin garin Cabo Rojo na kasar Puerto Rican, a daren ranar asabar ya same ta tana barci a kan shimfida, sannan ya watsa ma ta fetur a jiki ya banka mata wuta a wani abin da aka bayyana a matsayin laifin son rai.

Mahaifiyar wacce aka kashe, Nanette Camacho, ‘yar shekaru 34, ta samu kananan raunuka a fuskarta da hannayenta lokacin da take kokarin ceto ‘yarta. Kanin yarinyar mai shekaru tara shima ya kone yayin harin, amma raunin da ya samu ba na barazanar rai bane.

Da farko an kai yarinyar asibiti a lokacin da likitoci suka yi ma ta allurar kashe zafi, sannan suka mayar da ita zuwa wani asibiti.

Bonilla, wanda ya kasance a gida lokacin da ‘yan sanda suka zo don kama shi, an tuhume shi da laifuka bakwai, ciki har da zargin kisan kai uku.

Exit mobile version