Zamantakewa mu’amula ce da ke faruwa tsakanin mutane daban-daban. In aka ce zama ya hada ka da mutum to fa dole ka kasance mai abu biyu, Hakuri da Kauda kai.
Zama na aure zama ne da yake kunshe da kalubale mai dadi ko akasin haka, musamman in aka ce zama ya hada ka da uwa ko kuma wani dangi na miji. Da yawa mata suna daukan zama da uwar miji a matsayin wani zama mai tattara da kalubale wanda abun ba haka yake ba.
- Cutar Shakewar Numfashi Ta Kashe Mutum 25 A Jihar Kano
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Raunata Wasu A Katsina
Idan uwargida ta tsinci kanta a cikin matan da zama da uwar miji ya hada su to fa dole sai kin karo biyayya a kan wanda kike da shi, in aka ce biyayya ina nufin yanda uwargida za ta kalli mahaifanta haka ya kamata ta girmama na mijinta, yadda za ta yiwa iyayenta ladabi to su ma fa haka za ta yi musu.
Sannan uwargida ta kasance mai ihsani da kyautatawa tsakanin ta da uwar miji, idan uwar mijin na cin goro ta lazamci siya ta bata. Haka turare na jiki da na daki shi ma ta dan dinga siya tana ba ta ko ba kullum ba ko a wata sau daya.
Uwargida kar ki taba yarda ku raba tukunya da uwar mijinki, saboda yin haka yana kawo rabuwan kai sosai, in dai zaman gida ya hada uwsargida da sirika to ki daure ki kasance kina dafa abinci duka gida kuma kar ki kasance mai rowa ki zuba mata adadin da kika san zai ishe ta har ma wani bako ya zo ya ci, saboda yin hakan yana kara wa uwargida daraja da kima a idon sirikar ta da ma idon duniya baki daya. Kuma ko zaginta uwar mijin ta ji ana yi za ta so ta kare ta.
Uwargida ta kasance mai kauda kai ga abinda surukarta za ta yi ko ta ki yi. Kar uwargida ta ga an yi baki sun shige daki ta kwallafa rai sai ta kasa kunne ta ji me ake fada, ko kila tadinta ake yi, kar ki sake kiyi wannan za ki jiyo wa kanki abin da zai hana ki kwanciyar hankali, tun farko ma uwargida kar ta sa wa ranta wannan, ta sa wa zuciyar ta salama, ta sa wa ranta cewa in an yi baki a gidan to abin da ya dame su suke zantawa.
Kar uwargida ta kasance mai sa ido ga abinda Mijinta ya kawo wa mahaifiyarsa, ta kasance mai kauda kai domin kuwa hakan zai kara mata daraja da kima a idon shi. Duk abin da zai kawo kar ki ce ke ma fa dole sai an miki a’a ki kauda kai in akwai rabonki sai ki ga ke ma an kawo miki. Kuma yin hakan yana kara wa uwargida daraja da kima a idon kowa ma ba miji kadai ba.
Aikace-Aikacen gida kar uwargida ta dauka zaman uwar mijinta a kusa da ita wata dama ce da za ta dinga saka uwar miji aiki ko kadan hakan ba tarbiyya ba ce kuma babu dan da zai ga haka ya ji dadi. Ko da ita ta nemi ta tayaki ki nuna mata ita uwa ce lokacin hutunta ne saboda haka ta je ta huta za ki yi aikin.
Nuna wa Maigida ya kyautata wa uwarsa kar uwargida ta jira wai sai dole miji ya yi wa uwarsa a’a ke ma kamar idonsa kike a gidan saboda haka ki nuna masa duk wasu hanyoyin kyautata wa mahaifiya, ki dinga nuna masa wanda hakan zai kara miki kima da daraja sosai a idonsa.